Wata Babbar Kotun Tarayya da ke zama a Jihar Kaduna ta ɗage sauraron ƙarar neman beli da tsohon gwamnan jihar, Nasir El-Rufai, ya gabatar zuwa ranar 31 ga Maris, 2026.
An yanke wannan hukunci ne bayan zaman kotun da aka yi a ranar Talata, inda lauyoyin ɓangarorin biyu suka gabatar da hujjoji a gaban kotun.
A yayin zaman, lauyan wanda ake ƙara, Ukpon Akpan, ya roƙi kotun da ta ba wa wanda yake karewa beli, yana mai cewa wannan haƙƙinsa ne na kundin tsarin mulki, tare da buƙatar a ba shi damar shirya kansa yadda ya kamata domin kare kansa.
Sai dai ɓangaren masu ƙara sun yi adawa da wannan buƙata, suna masu cewa zarge-zargen da ake yi wa El-Rufai suna da matuƙar nauyi, kuma bayar da beli na iya kawo cikas ga binciken da ake ci gaba da yi.
ƙarin bayani nan tafe……..

