Kasuwar hannayen jari ta Najeriya ta samu gagarumin tashin gwauron zabo a makon da ya gabata, bayan wani muhimmin sauyi na doka da Hukumar Fansho ta Ƙasa ta yi, wanda ya bai wa asusun fansho damar ƙara yawan jarin da suke zubawa a hannayen jari.
Hukumar Fansho ta Ƙasa, National Pension Commission (PenCom), ta amince da ƙara iyakar zuba jari a hannayen jari ga Masu Gudanar da Asusun Fansho (PFAs), lamarin da ya jawo sayayya mai yawa musamman a manyan kamfanoni da matsakaitan kamfanoni.
Sakamakon haka, babban ma’aunin kasuwa na Nigerian Exchange Limited (NGX) wato All-Share Index ya ƙaru da kashi 6.16 cikin ɗari, inda ya kai maki 182,313.08. Hakan ya ƙara darajar kasuwa da Naira tiriliyan 6.79, wanda ya kai jimillar darajar kasuwar zuwa Naira tiriliyan 117.03.
Cinikayya Ta Kai Matakin Tarihi
Jimillar cinikayya ta kai hannayen jari biliyan 4.65 da darajarsu ta kai Naira biliyan 193.33, idan aka kwatanta da biliyan 3.86 da darajarsu ta kai Naira biliyan 128.58 a makon da ya gabata.
Tashin farashin ya shafi kusan dukkan sassa na kasuwa. Bangaren Man Fetur da Iskar Gas ya samu ƙaruwa da kashi 11.40 cikin ɗari, inda Seplat Energy ya ƙaru da kashi 13.98, yayin da Aradel Holdings ya samu kashi 10.78.
Bangaren Kayayyakin Masana’antu ya tashi da kashi 7.09 cikin ɗari, sakamakon hauhawar farashin Lafarge Africa da kashi 12.87, da kuma Dangote Cement da kashi 6.81.
A bangaren bankuna kuwa, an samu ƙaruwa da kashi 5.84 cikin ɗari, yayin da Kayayyakin Mabukaci suka ƙaru da kashi 2.95, sakamakon tashin farashin Nestle Nigeria da kashi 21, da Dangote Sugar Refinery da kashi 20.77.
Kamfanonin da Suka Fi Yin Riba
Sabon kamfani mai suna Zichis ne ya jagoranci masu riba, inda farashinsa ya ƙaru da kashi 60.71 cikin ɗari. Sai Union Dicon Salt da kashi 60.15, da kuma Daar Communications da kashi 55.26.
A ɓangaren masu asara kuwa, Abbey Mortgage Bank ne ya fi faduwa, inda ya sauka da kashi 26.42 cikin ɗari sakamakon sayar da riba (profit-taking).
Hasashen Makon Gaba
Bangaren Harkokin Kuɗi ne ya fi kowa yawan cinikayya, inda ya kai kusan kashi 60 cikin ɗari na jimillar cinikayya, da hannayen jari biliyan 2.78 da darajarsu ta kai Naira biliyan 74.06.
Jimillar kamfanonin da suka samu ƙaruwa sun kai 79, yayin da 27 suka fuskanci faduwa — alamar kyakkyawan yanayin kasuwa.
Masu nazari sun yi hasashen cewa za a iya samun yanayi mai gauraya a makon da ke tafe. Kamfanin AIICO Capital ya ce ana sa ran za a samu gaurayen yanayi yayin da PFAs ke daidaita jarinsu zuwa kamfanonin da ke da tushe mai ƙarfi, duk da yiwuwar sayar da riba bayan tashin da aka samu.
Haka kuma, Cowry Asset Management ya bayyana cewa sayayya sakamakon yawan kuɗin da ke zagayawa a kasuwa zai iya ci gaba da tallafa wa kasuwar, sai dai ana iya fuskantar ɗan ja da baya.
Kamfanin ya ƙara da cewa, “Yanayin kasuwa zai dogara ne kan ci gaba da shiga manyan masu zuba jari da kuma sauyin sassa (sector rotation) a kasuwa.”
