Gwamnatin Tarayya Ta Samu ₦55.5trn Daga Sayar da Danyen Mai a 2025

Najeriya ta samu matsakaicin kuɗi har ₦55.5 tiriliyan daga sayar da danyen mai a shekarar 2025, kamar yadda wani bincike da ya dogara da alkaluman samarwa na hukuma daga Hukumar Kula da Harkokin Man Fetur ta Sama (NUPRC) da kuma bayanan farashin danyen mai da Babban Bankin Najeriya (CBN) ya nuna.

Adadin kuɗin da aka samu a 2025 ya fi na shekarar 2024, inda a wancan shekarar aka samu kimanin ₦50.88 tiriliyan daga sayar da danyen mai.

Bayanan NUPRC sun nuna cewa Najeriya ta samar da jimillar ganga miliyan 530.41 na danyen mai daga watan Janairu zuwa Disamba 2025. Samarwar ta yi ta sauyawa a tsawon shekarar sakamakon matsalolin tangarda, cikas a ayyukan hakar mai, da kuma fara murmurewa a wasu rijiyoyin mai.

An ƙiyasta kuɗin ₦55.5 tiriliyan ne ta hanyar ninka jimillar gangar danyen mai miliyan 530.41 da matsakaicin farashin ganga ɗaya na danyen mai, wato dala $72.08 a 2025, sannan aka maida dalar zuwa naira da canjin ₦1,450 kan dala ɗaya.

Samar da danyen mai ta fara da ƙarfi a farkon shekarar, inda aka samar da ganga miliyan 47.70 a watan Janairu, kafin ta faɗi zuwa ganga miliyan 41.02 a watan Fabrairu. A watan Maris, samarwar ta ɗan murmure zuwa ganga miliyan 43.42, sannan ta ƙaru zuwa ganga miliyan 44.57 a Afrilu. A zangon biyu na shekarar, samarwar ta kasance kusan daidaitacciya, inda ta kai ganga miliyan 45.04 a Mayu da kuma ganga miliyan 45.16 a Yuni.

A zangon uku na shekarar, samar da mai ya ƙaru zuwa ganga miliyan 46.73 a Yuli, amma ya sake raguwa zuwa ganga miliyan 44.47 a Agusta, sannan ya ƙara faɗuwa zuwa ganga miliyan 41.69 a Satumba, wanda ke daga cikin mafi ƙanƙantar adadin da aka samu a shekarar. Sai dai samarwar ta sake farfaɗowa a zangon ƙarshe, inda ta kai ganga miliyan 43.44 a Oktoba, ganga miliyan 43.08 a Nuwamba, da kuma ganga miliyan 44.08 a Disamba, a cewar NUPRC.

Duk da cewa samarwar ta kasance ƙasa da kaso da Najeriya ke da shi a OPEC a mafi yawan shekarar, farashin danyen mai ya taimaka wajen tallafa wa kuɗaɗen shiga. Bayanai daga CBN sun nuna cewa Bonny Light, nau’in danyen mai mafi muhimmanci a Najeriya, ya sayu da tsada a farkon shekarar kafin farashinsa ya ragu a zangon biyu.

A watan Janairu 2025, farashin Bonny Light ya kai matsakaicin dala $80.76 kan ganga ɗaya, kafin ya ragu zuwa $77.08 a Fabrairu da kuma $74.44 a Maris. Farashin ya ƙara faɗuwa a Afrilu zuwa $69.07, sannan ya kai ƙananan matsayi a Mayu da $65.90, sakamakon sauyin yanayin kasuwar man fetur ta duniya.

Sai dai farashin ya sake tashi a Yuni zuwa $73.50, kuma ya kasance kusan daidaitacce a zangon uku, inda ya kai matsakaicin $73.18 a Yuli, $70.55 a Agusta, da kuma $70.20 a Satumba, kafin ya sake raguwa zuwa $66.15 a Oktoba, wanda shi ne watan ƙarshe da CBN ta fitar da bayanai a kai.

Ta amfani da matsakaicin sauƙaƙen farashin Bonny Light na watanni 10 da CBN ta wallafa, an samu matsakaicin farashin dala $72.08 kan ganga ɗaya a lokacin da ake nazari.

Idan aka yi amfani da wannan matsakaicin farashi kan jimillar gangar danyen mai miliyan 530.41 da Najeriya ta samar, an ƙiyasta cewa kuɗaɗen shiga na danyen mai a 2025 sun kai kusan dala biliyan $38.23. Idan aka maida wannan adadi zuwa naira da canjin ₦1,450 kan dala ɗaya, hakan ya kai kimanin ₦55.5 tiriliyan a kuɗaɗen shigar danyen mai na shekarar.

Masana harkar man fetur sun bayyana cewa wannan adadi na wakiltar kuɗin shiga gaba ɗaya (gross revenue) ne, ba wai ainihin kuɗin da gwamnati ta karɓa kai tsaye ba, domin bai haɗa da kuɗaɗen samarwa, kudaden haɗin gwiwar kamfanoni (JV cash calls), maidowa kuɗaɗen kwangilar rabon samarwa (PSC cost recovery), satar mai, wajibcin samar da danyen mai cikin gida, ko kuma jinkirin ɗaukar mai ba.

Duk da haka, wannan bincike ya nuna a sarari girman kuɗaɗen shigar da aka samu daga danyen mai a shekarar, bisa bayanan hukuma na samarwa daga NUPRC da kuma ma’aunin farashi daga CBN, tare da jaddada muhimmancin daidaiton samarwa da kyakkyawan farashi ga tattalin arziƙin Najeriya da ke dogaro da mai.

Ya kamata a lura cewa adadin ₦55.5 tiriliyan shi ne kuɗin da ake sa ran Kamfanin Man Fetur na Ƙasa na Najeriya (NNPCL), kamfanonin mai na ƙasashen waje, da kuma na cikin gida suka samu daga sayar da danyen man da aka samar a Najeriya.

A shekarar 2024 kuwa, an ruwaito cewa Najeriya ta samar da ganga miliyan 408.68 na danyen mai, inda hakan ya samar da kimanin ₦50.88 tiriliyan.