Gwamnatin Jihar Enugu ta tabbatar da barkewar cutar haukan kare (rabies) a ƙaramar hukumar Igbo Etiti, tare da gargadin mazauna yankin kan hatsarin mutuwar da cutar ke haifarwa.
Kwamishinan Noma na jihar, Patrick Ubru, ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa ga jama’a, inda ya bukaci a yi taka-tsantsan, yana mai cewa cutar rabies cuta ce ta ƙwayar virus wadda ke shafar dabbobi da mutane, kuma ana kamuwa da ita ne galibi ta hanyar cizon kare ko yawu daga dabba mai ɗauke da cutar.
Ya jaddada cewa da zarar alamomin cutar sun bayyana, rabies “kusan koyaushe tana kashe mai kamuwa da ita,” lamarin da ya sa gwamnati ta fara ɗaukar matakan dakile yaduwar cutar.
Sanarwar ta ce, “Ana kira ga duk masu kiwon karnuka da sauran dabbobi da su gaggauta yi musu allurar rigakafin rabies ba tare da ɓata lokaci ba,” tare da ƙara da cewa dole ne a killace dabbobi a hana su yawo a waje ba tare da kulawa ba.
Haka kuma, an shawarci mazauna yankin da su guji hulɗa da karnukan da ba su da mai, tare da kai rahoton duk wata dabba da ke nuna alamun tashin hankali, zubar yawu da yawa, halayen da ba su saba ba, ko shanyewar jiki ga hukumomin likitocin dabbobi.
Ma’aikatar ta kuma bayyana matakan gaggawa ga waɗanda suka fuskanci cizo ko rauni daga dabba, inda ta ce, “Duk wanda dabba ta cije ko ta goge shi, ya kamata ya wanke wurin da kyau da sabulu mai laushi a ƙarƙashin ruwa mai gudana na akalla mintuna 10, sannan ya garzaya asibiti cikin gaggawa.”
Ubru ya tabbatar da cewa Sashen Kula da Lafiyar Dabbobi na jihar na aiki tare da masu ruwa da tsaki domin dakile yaduwar cutar, yayin da aka bukaci shugabannin al’umma su wayar da kan jama’a kan haɗarin rabies.
Gwamnatin ta jaddada cewa wayar da kai da kuma kai rahoton duk wata alama cikin gaggawa na da matuƙar muhimmanci wajen hana asarar rayuka, tare da umartar a kai rahoton duk wani zargi ga Sashen Kula da Lafiyar Dabbobi na jihar.
