Gwamnan Jihar Kebbi, Nasir Idris, a ranar Alhamis ya dakatar da Kwamishinan Lafiya na jihar, Yunusa Musa Ismail, bisa sakaci wajen aiki da kuma raina nauyin da aka dora masa.
Dakatarwar ba za ta rasa nasaba ba da ce-ce-ku-cen da ya biyo bayan cafke wani mutumi, Hassan Mai-Waya Kangiwa, wanda aka kama saboda ya wallafa a kafafen sada zumunta bidiyon da ke nuna halin rashin kyau da Asibitin Gwamnati na Kangiwa ke ciki.
Gwamnatin jihar ta dora alhakin kamun kan wani jami’in karamar hukuma da ta ce ya wuce gona da iri, amma gwamnan ya bada umarnin dakatar da kwamishinan lafiya na jihar nan take.
Wata sanarwa da mai bai wa gwamnan shawara na musamman kan harkokin yada labarai, Yahaya Sarki, ya fitar ta bayyana cewa an umurci kwamishinan da ya bayar da kwararan dalilai kan dalilin da yasa ba a dauki matakin ladabtarwa a kansa ba saboda sakacin da ya yi wajen sauke nauyin da ke wuyansa.
Sanarwar ta kara da cewa gwamnan ya jaddada kudirin gwamnatinsa na gudanar da mulki bisa gaskiya, ladabi da ingantaccen isar da ayyuka ga jama’ar jihar.
Kwamishinan Yaɗa Labarai na jihar, Yakubu Ahmed Birnin Kebbi, wanda ya yi magana a madadin gwamnatin jihar, ya ce Gwamna Nasir Idris ya bada umarnin a saki mutumin daga ofishin ’yan sanda inda aka tsare shi.
Ya ce: “Bidiyon tsofaffin hotunan asibitin ne, amma aka baza su a shafukan sada zumunta da gangan domin su bata kyawawan ayyukan da gwamnatin yanzu ke yi a jihar.”
Kwamishinan ya kara da cewa dukkan manyan asibitocin jihar suna cikin yanayi mai kyau, yana mai jaddada cewa: “Mun fahimci ana baza tsofaffin bidiyon asibitocin ne kawai domin a bata sunan wannan gwamnati.”
