Trends

Gwamna Yusuf ya Fice Daga Jam’iyyar NNPP

Kabir Abba Yusuf gwamnan Jihar Kano

Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya sanar da ficewarsa daga jam’iyyar New Nigeria People’s Party (NNPP), yana mai danganta matakin da rikice-rikicen cikin gida da kuma takaddamar shugabanci da ke kara kamari a cikin jam’iyyar.

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da kakakin gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya fitar a ranar Juma’a.
A cewar sanarwar, gwamnan ya mika takardar murabus dinsa ga Shugaban NNPP na Mazabar Diso-Chiranchi da ke Karamar Hukumar Gwale, inda murabus din zai fara aiki daga ranar 25 ga Janairu, 2026.

“Ina rubuto wannan wasika ne da cike da godiya domin sanar da shugabancin jam’iyyar New Nigeria People’s Party (NNPP) game da matakina na ficewa daga jam’iyyar,” in ji gwamnan a cikin wasikar.

Gwamna Yusuf ya nuna godiyarsa ga jam’iyyar bisa damar da ta ba shi da kuma goyon bayan da ya samu daga shugabanni da mambobinta a fadin Jihar Kano.

“Ina matukar godiya ga damar da jam’iyyar, shugabancinta da mambobinta a fadin Jihar Kano suka ba ni tun daga shekarar 2022, da kuma goyon baya, kyakkyawar mu’amala da hadin kai da na samu a tsawon lokacin da nake cikinta,” in ji shi.

Sai dai gwamnan ya bayyana cewa rikice-rikicen cikin gida da shari’o’i da dama da ke gaban kotuna sun zama babban dalilin yanke shawarar tasa.
“A baya-bayan nan, jam’iyyar ta fuskanci kalubale masu tsanani sakamakon sabanin shugabanci da kuma shari’o’i da dama da ke gaban kotuna domin yanke hukunci,” in ji shi.

Ya kara da cewa rikicin ya haifar da rashin jin dadin mambobi, rarrabuwar kai da kuma raunana dunkulewar jam’iyyar a matakin jiha da kasa baki daya.

“Karuwar rashin jin dadin mambobi ya haifar da rarrabuwar kai mai zurfi a cikin jam’iyyar, wanda ke nuna alamun da ba sa saukin warwarewa, tare da haifar da rashin tabbas a matakin jiha da kasa,” Yusuf ya bayyana.

Gwamnan ya ce ya dauki matakin ne bayan dogon tunani, domin kare muradun al’ummar Jihar Kano.

“Bayan yin nazari sosai, kuma ba tare da nuna shakku kan ikon jam’iyyar na warware matsalolinta ba, na yanke shawarar cewa ficewata ita ce mafi alheri ga al’ummar Jihar Kano,” in ji shi.
Ya jaddada cewa ya dauki matakin cikin gaskiya da lumana, ba tare da wata gaba ko bacin rai ba, yana mai tabbatar da aniyarsa ta ci gaba da aiki domin zaman lafiya, hadin kai da ci gaban jihar.

A halin da ake ciki kuma, sanarwar ta bayyana cewa ficewar gwamnan ta zo ne tare da ta ‘yan Majalisar Dokokin Jihar Kano 21, ‘yan Majalisar Wakilai takwas, da kuma shugabannin kananan hukumomi 44 a fadin jihar.

Sakataren NNPP na Mazabar Diso-Chiranchi, Hon. Kabiru Zubairu, wanda ya tabbatar da karbar takardar murabus din gwamnan, ya yaba da irin rawar da Gwamna Yusuf ya taka a lokacin mulkinsa.

“Ina goyon bayan matsayar Mai Girma Gwamna kan rikicin da ke addabar jam’iyyarmu. Duk da kokarin da muke yi na shawo kansa, ba mu da wani zabi face karbar murabus din daya daga cikin gwamnonin NNPP mafi kokari,” in ji Zubairu.

Ya kuma yaba wa gwamnan bisa manyan ayyukan da ya ce ya yi a bangarorin ababen more rayuwa, gyaran birane, kiwon lafiya, ilimi da kuma bunkasa tattalin arziki.