Trends

E-Sakamako Zabe: Obi Ya Jagoranci Masu Zanga-zanga Zuwa Majalisar Ƙasa

Tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa a zaɓen 2023 ƙarƙashin jam’iyyar Labour Party, Peter Obi, ya jagoranci masu zanga-zanga zuwa Majalisar Ƙasa, kan batun watsa sakamakon zaɓe kai tsaye ta hanyar lantarki.

Dan siyasar, wanda ke tare da dimbin magoya bayansa ciki har da fitacciyar ’yar gwagwarmaya Aisha Yesufu, a halin yanzu yana bakin ƙofar ginin majalisar dokokin ƙasar.

“Muna shan wahalar barazana. Ba ma son wata matsala ko tangarda kuma. Muna so komai ya tafi daidai. A bar zaɓe ya bi tsarin da ya dace. Duk wanda ya yi nasara, za mu amince,” in ji Obi.
Ya ƙara da cewa, “To me ya sa ake kawo wannan rikice-rikice?”

Masu zanga-zangar sun hallara ne domin neman amincewa da watsa sakamakon zaɓe kai tsaye ta lantarki daga rumfunan zaɓe, a matsayin tilas, a cikin Kudirin Gyaran Dokar Zaɓe (Electoral Amendment Bill) da Majalisar Ƙasa ke duba.

Jami’an tsaro, musamman ’yan sanda tare da Nigerian Security and Civil Defence Corps (NSCDC) da sauran hukumomin tsaro na paramilitary, sun jibge motocinsu a yankin, yayin da jami’ansu suka rufe muhimman wurare domin tabbatar da zaman lafiya da tsaro.

Rikice-rikice da muhawara sun ci gaba da biyo bayan gyaran Dokar Zaɓe da ake yi gabanin babban zaɓen 2027, musamman kan batun watsa sakamakon zaɓe kai tsaye ta hannun Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta (INEC).

Yayin da ’yan Najeriya da dama ke kira ga ’yan majalisa da su sanya watsa sakamakon zaɓe ta lantarki a matsayin dole, wasu ’yan majalisar na ganin cewa ya kamata a bar batun a matsayin zaɓi (discretionary) ga INEC.