Trends

Tinubu Ya Saka Wa ‘Yan Wasan Super Falcons da Dala Dubu dari, Lambar Yabo, da Gidaje

Yan Wasan Super Falcons a Fadan Shugaban Kasa

Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, ya bai wa ‘yan wasan Super Falcons kyautar dala $100,000 kowannensu, lambar girmamawa ta Officer of the Order of the Niger (OON), da kuma gida guda uku-ɗaki a birnin tarayya Abuja.

Wannan girmamawa da kyautar ta zo ne a ranar Lahadi, 28 ga Yuli, a matsayin yabo ga nasarar da tawagar Super Falcons ta samu a gasar 2024 Women’s African Cup of Nations da aka gudanar a Rabat, ƙasar Maroko.

Tawagar yan wasa guda 24, ƙarƙashin jagorancin ƙapitan su Rasheedat Ajibade, sun lashe kofin karo na 10, bayan sun doke ƙasar Maroko a wasan karshe da aka buga a ranar 27 ga Yuli.

Mai taimakawa Shugaban kasa kan harkokin kafafen sada zumunta, Olusegun Dada, ya bayyana hakan a shafinsa na X (tsohon Twitter) da aka tantance. Ya ce kowanne daga cikin ‘yan wasan za su karɓi dala $100,000 da gida mai ɗakuna uku a Renewed Hope Estate.

Haka kuma, ya ce kowanne daga cikin mambobin kwamitin fasaha na Super Falcons za su samu kyautar dala $50,000.

Dada ya rubuta cewa:
“Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya bai wa ‘yan wasan Super Falcons lambar girmamawa ta Officer of the Order of the Niger (OON), gida mai ɗakuna uku kowannensu, da kuma kyautar dala $100,000 ga kowanne ɗaya daga cikin ‘yan wasan 24. Ya kuma bai wa mambobin kwamitin fasaha kyautar dala $50,000 kowannensu.”

Wannan na cikin kokarin gwamnati na nuna godiya da girmamawa ga jarumtar ‘yan wasan kasar da suka sake tabbatar da bajintar Najeriya a fagen kwallon kafa.

One thought on “Tinubu Ya Saka Wa ‘Yan Wasan Super Falcons da Dala Dubu dari, Lambar Yabo, da Gidaje

Comments are closed.