Hukumar gudanarwar makarantar HHH Foundation School ta nuna matukar jin dadinta da godiya ga dukkan masu ruwa da tsaki – ciki har da malamai, iyaye da dalibai – saboda gudummawar da suke bayarwa wajen tabbatar da ci gaban makarantar da kuma sanya ta zama abin koyi a fagen ilimi.
Daraktan makarantar, Malam Ahmad Al-Qasseem, ne ya bayyana hakan a jawabinsa na bude taron jawabi da bayar da lambobin yabo da aka gudanar a ranar Asabar a Abdulsalami Abubakar Multipurpose Hall, Base University, a Babban Birnin Tarayya (FCT), Abuja.
“Ina so in yi amfani da wannan dama in karfafa gwiwar kowa da kowa da mu kara kokari domin ganin cewa makarantar tana da karfin tallafa wa dalibai da wadanda suka ci lambar yabo a irin wannan biki.”
“Ga ku da kuka nuna jajircewa a fannin karatu da tarbiyya da kuma harkokin waje, nasararku shaida ce ga goyon bayan da malamanku da iyayenku suka bayar. Allah ya kara muku ilimi, hikima da kyawawan halaye yayin da kuke ci gaba zuwa ajujuwa masu gaba,” in ji shi.
Daraktan ya kuma jaddada mahimmancin ayyukan ci gaban al’umma da daliban makarantar ke aiwatarwa, inda ya bayyana cewa dalibai sun gudanar da gagarumin aiki a jarrabawar shiga manyan makarantu (common entrance), inda dalibai da dama suka samu matsakaicin maki na kashi 70 cikin dari.
“Zaku ga wasu daga cikin ayyukan da dalibai suka gudanar a yau yayin da za su gabatar da ayyukansu. Dalibanmu na matakin firamare sun yi fice a jarrabawar shiga manyan makarantu. Har ila yau, sun halarci gasar ƙasa ta Kungiyar Lissafi ta Najeriya (Mathematical Association of Nigeria Olympiad),” in ji shi.
Ya kuma roki iyaye da su ci gaba da nuna jajircewa wajen biyan kudin makaranta akan lokaci duk da kalubalen tattalin arzikin da ake fuskanta.
“Iyaye su tabbatar da cewa suna biyan kudin makaranta akan lokaci. Kodayake tattalin arzikin yana da wahala, amma muna so mu jaddada cewa biyan kudade akan lokaci yana da matukar muhimmanci wajen tafiyar da ayyukan makaranta.”
Wani uba daga cikin mahalarta, Umar Zubairu, ya nuna farin cikinsa bayan diyarsa, Alisha Umar Zubairu, ta samu matsayi na biyu (matakin Diamond), inda ya ce, “Ina godiya ga Allah Madaukakin Sarki saboda ni’imar rayuwa da wannan lambar yabo.”
Daga cikin abubuwan da suka dauki hankalin mahalarta a taron akwai gabatarwar musamman daga daliban makarantar sakandare, inda suka nuna yadda za a yi amfani da fasahar wucin gadi (AI) wajen sarrafa kayan lantarki a gida da kuma kula da hasken wucewa (traffic light).
An rufe taron ne da bayar da kyaututtuka ga malamai da dalibai wadanda suka nuna bajinta a harkar karatu da tarbiyya.
