Trends

Gwamnatin Gombe Ta Biya Bashin Fansho Na Naira Biliyan 25.6 Ga Tsofaffin Ma’aikatan LG

Gwamnan Gombe Inuwa Yahaya

Gwamnatin Jihar Gombe ta bayyana cewa a cikin shekaru shida da suka gabata, ta biya sama da naira biliyan 25 a matsayin hakkokin fansho ga tsofaffin ma’aikata na jiha da na kananan hukumomi a fadin Kananan Hukumomi 11 na jihar.

Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya ne ya bayyana hakan a wajen kaddamar da sabon zagaye na biyan bashin fansho da ya jibanci tsofaffin ma’aikatan kananan hukumomi na jihar, wanda aka gudanar a fadar gwamnati da ke Gombe.

A jawabinsa, Gwamna Yahaya ya sake jaddada kudirin gwamnatinsa na biyan dukkan hakkokin da ake bin tsofaffin ma’aikata tsawon shekaru fiye da goma, a matakin jiha da kuma na kananan hukumomi.

Ya bayyana cewa tun bayan hawansa mulki a 2019, gwamnatinsa ta biya sama da naira biliyan 25 ga ma’aikatan da suka yi ritaya daga aiki a matakin jiha da kananan hukumomi.

A cewarsa:
“A cikin shekaru shida da suka gabata, mun raba naira biliyan 23.566 a matsayin bashin fansho. Da wannan karin biyan da muka yi yau na NGN2,060,337,466.45, hakan na nufin mun kai adadin tarihi na Naira biliyan 25.626 da aka biya daga 2019 zuwa yanzu.”

Ya kara da cewa lokacin da suka hau mulki a 2019, sun gaji bashin fansho na sama da naira biliyan 21 da ake bin gwamnati, wanda ya kasance wani babban kalubale ga tsofaffin ma’aikatan jihar.

“Kananan hukumomi ba su iya biyan albashi ba ko aiwatar da ayyuka na yau da kullum. Daga 2013 zuwa 2019, gwamnatin da ta gabata tana ciwo bashi don biyan albashi,” in ji Gwamnan.

Yahaya ya bayyana cewa gwamnati za ta ci gaba da biyan bashin fansho a kowane wata ta hanyar tsara kudade da sarrafa su yadda ya dace, tare da nufin kawo karshen duk wani bashi da ake bi gwamnati daga yanzu zuwa shekara ta 2027.

Ya kuma bayyana tsarin biyan fanshon a matsayin mai adalci, inda kowace karamar hukuma za ta biya bisa ga karfin tattalin arzikinta.

Ya ce:

  • Kwami, Nafada da Funakaye za su biya wadanda suka yi ritaya a 2023.
  • Akko, Billiri da Shongom za su biya wadanda suka yi ritaya a 2016 da 2017.
  • Dukku za ta biya na shekarar 2016.
  • Balanga za ta biya wadanda suka yi ritaya a 2015 da 2016.
  • Gombe da Kaltungo za su biya na 2014 da 2015.
  • Yamaltu Deba za ta biya na 2015.

Tun da farko, Auditor-General na jihar kuma Shugaban Kwamitin Biyan Fansho, Muhammad Buba Gombe, ya bukaci wadanda suka amfana da kudaden su yi amfani da su cikin hikima domin inganta rayuwarsu bayan ritaya da kuma bada gudunmawa ga ci

One thought on “Gwamnatin Gombe Ta Biya Bashin Fansho Na Naira Biliyan 25.6 Ga Tsofaffin Ma’aikatan LG

  1. — Monica – Your Ultimate AI Assistant for Every Task!
    Looking for a way to boost productivity and streamline your daily tasks? Monica.im is your all-in-one AI assistant, integrating top-tier AI models like OpenAI o1-preview, GPT-4o, Claude 3.5, and Gemini 1.5. It helps you with communication, research, writing, and even coding—all accessible through a browser extension for Chrome and Edge, as well as mobile apps for Android and iOS. (monica.im)

    — Key Features of Monica (https://monica.im/invitation-affiliate?ref=ztk2ymi&ref_aff=ztk2ymi

    AI Chat: Interact with leading AI models in one place.
    AI Summarizer: Save up to 90% of your time by instantly summarizing web pages and videos.
    AI Writer: Generate or enhance any content 10x faster, from short paragraphs to full-length articles.
    AI Search: A powerful search engine with real-time access to the latest information.
    AI Translator: Translate entire web pages for seamless bilingual reading.
    AI Art Generator: Turn your ideas into stunning images effortlessly.

    — Why Choose Monica?

    Available Across All Platforms: Use Monica on browsers, desktops, or mobile devices.
    Intelligent Toolbar: Quickly explain, translate, or summarize any highlighted text.
    Writing Assistant: Create, rewrite, or improve text content on any webpage.
    Enhanced Web Experience: Get AI-powered answers alongside search results, summarize YouTube videos, and extract key insights with timestamps.
    — Start Boosting Your Productivity Today with Monica https://monica.im/invitation-affiliate?ref=ztk2ymi&ref_aff=ztk2ymi)

    — Install for Free: https://monica.im/invitation-affiliate?ref=ztk2ymi&ref_aff=ztk2ymi

Comments are closed.