Ciwon Daji: Gwamnatin Tarayya Ta Kaddamar da Cibiyoyi Uku a Nigeriya

Cutar Daji

Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta kammala gina sabbin cibiyoyi uku na zamani domin kula da masu fama da cutar daji (cancer) a sassa daban-daban na kasar.

Cibiyoyin suna cikin manyan asibitoci ne kamar haka: Asibitin Koyarwa na Jami’ar Benin (UBTH) a Benin, Asibitin Koyarwa na Tarayya a Katsina, da kuma Asibitin Koyarwa na Jami’ar Najeriya da ke Enugu.

Wannan ci gaba ya kasance ne bisa sanarwar da Ministan Watsa Labarai da Tsare-Tsaren Wayar da Kai na Kasa, Mohammed Idris, ya wallafa a shafinsa na X (tsohon Twitter) a ranar Alhamis.

Ministan ya bayyana hakan ne yayin da ya halarci bikin kaddamar da daya daga cikin cibiyoyin a Katsina tare da Ministan Lafiya da Walwalar Jama’a, Muhammad Ali Pate, da Ministan Kudi kuma Shugaban Tsare-Tsaren Tattalin Arziki, Wale Edun.

Ya ce, “Shirin sabunta fannin lafiya na Shugaba Bola Ahmed Tinubu na kawo sauyi a fadin Najeriya. Alkawurran da aka dauka suna samun cika!”

A cewarsa: “Gwamnatin Tarayya ta kammala aikin gina cibiyoyi uku na zamani domin kula da marasa lafiya masu fama da cutar daji a Benin (Asibitin Koyarwa na Jami’ar Benin), Katsina (Asibitin Koyarwa na Tarayya, Katsina), da Enugu (Asibitin Koyarwa na Jami’ar Najeriya).”

“Yau na kasance tare da abokan aikina Ministocin Lafiya da Kudi domin kaddamar da wadannan muhimman ayyuka, inda muka fara daga cibiyar da ke Katsina,” in ji shi.

Ministan ya kuma bayyana cewa wadannan cibiyoyi guda uku na daga cikin matakin farko na gina sabbin cibiyoyi guda shida na maganin cutar daji a manyan asibitocin koyarwa na tarayya a fadin kasar.

An aiwatar da wadannan ayyuka ne da hadin gwiwar Hukumar Zuba Jari ta Kasa (NSIA).