Nentawe Ya Zama Shugaban Jam’iyyar APC

Prof. Nentawe, Shugaban Jam’iyyar APC

Ministan Harkokin Jin Kai da Yaki da Talauci, Farfesa Nentawe Yilwatda, an tabbatar da shi a hukumance a matsayin sabon shugaban jam’iyyar All Progressives Congress (APC) na kasa.

An mika sunansa domin shugabancin jam’iyyar ta APC daga Gwamnan Jihar Imo, Hope Uzodimma, inda Kakakin Majalisar Wakilai ta Tarayya, Hon. Tajudeen Abbas, ya mara masa baya. Bayan amincewa da sunansa, an rantsar da shi nan take domin fara gudanar da aikinsa.

Rahotanni da dama sun nuna cewa Nentawe ne babban dan takara da ya fi samun goyon baya daga cikin ‘yan jam’iyyar domin wannan mukami tun kafin lokacin zabensa.

Nentawe dan asalin Jihar Filato ne, daga yankin Arewa ta Tsakiya — yanki da aka ware domin samar da shugaban jam’iyyar kafin nada tsohon gwamnan Jihar Kano, Dr. Abdullahi Umar Ganduje, wanda ya ajiye mukaminsa a farkon wannan wata.

Tursasawa da matsin lamba daga cikin jam’iyyar, musamman daga jiga-jigan Arewa ta Tsakiya, ya sanya aka nemi sabon shugaban jam’iyyar, bayan Ganduje ya yi murabus. Wannan na zuwa ne bayan korafin da suka yi dangane da yadda aka cire Sanata Abdullahi Adamu daga kujerar shugabancin jam’iyyar bayan kammala zaben 2023 da ya bai wa Bola Ahmed Tinubu nasara a matsayin Shugaban Kasa.