Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta bukaci gwamnatocin kasashen Afirka, ma’aikatan lafiya da al’umma da su kara kaimi wajen inganta bayar da jini na son rai tare da fadada damar samun ingantaccen jini da kayayyakin jini masu tsaro.
Daraktan WHO na Yankin Afirka, Farfesa Mohamed Janabi, ya bayyana hakan a sakon da ya fitar domin bikin Ranar Masu Ba da Jini ta Duniya ta shekarar 2026, mai taken “Ɗigon Ɗan Adam Daya: Ka Ba da Jini, Ka Ceci Rayuka.”
Janabi ya bayyana bayar da jini a matsayin aiki na tausayi da hadin kai wanda ke ceton rayuka marasa adadi a kullum.
Ya ce dubban marasa lafiya a fadin Afirka na dogaro da karin jini, ciki har da mata masu fuskantar matsalolin haihuwa, yara masu fama da zazzabin cizon sauro mai tsanani da karancin jini, wadanda suka samu raunuka a hadurra, da kuma masu fama da cututtuka na dindindin.
“Ingantaccen jini da kayayyakin jini na daga cikin muhimman ginshikan tsarin lafiya mai dorewa, kuma suna da matukar muhimmanci wajen cimma burin samar da lafiya ga kowa a nahiyar,” in ji shi, yayin da ya yaba wa masu bayar da jini na son rai, yana mai kiran su masu ceton rayuka da gudummawarsu ke karfafa al’umma.
WHO ta bayyana cewa an samu ci gaba a fannin bayar da jini, inda adadin gudummawar jini ya karu daga miliyan 2.2 a farkon shekarun 2000 zuwa kusan miliyan bakwai a shekarar 2023, yayin da kusan kashi 70 cikin 100 na jinin ke fitowa daga masu bayarwa na son rai.
Sai dai duk da wannan ci gaba, Janabi ya yi gargadin cewa har yanzu akwai gibi mai yawa, inda Afirka ke samun gudummawar jini shida kacal a cikin mutane 1,000, adadin da ya yi kasa da bukatun tsarin lafiya.
Ya jaddada muhimmancin cikakken gwajin jini domin gano cututtuka kamar HIV, hanta (hepatitis) da cutar syphilis, tare da amincewa cewa har yanzu akwai gibin da ya kamata a cike.
Daraktan ya kuma yi kira da a ci gaba da zuba jari a shirye-shiryen samar da jini na kasa, da karfafa kayayyakin more rayuwa, da wayar da kan jama’a, tare da kara sa hannun al’umma domin rage gibin da ke tsakanin bukata da wadatar jini.
Janabi ya bukaci duk wadanda suka cancanta su rika bayar da jini akai-akai, yana mai cewa kowace gudummawar jini na kawo fata, mutunci da kuma kyakkyawar makoma ga masu bukatarsa.
