Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar African Democratic Congress (ADC), Atiku Abubakar, ya zabi tsohon Ministan Sufuri, Chibuike Amaechi, a matsayin abokin takararsa na mataimakin shugaban kasa.
Wata majiya ta kusa da Amaechi da ta nemi a sakaya sunanta ta tabbatar da hakan, tana mai cewa tsohon gwamnan jihar Rivers na wa’adi biyu ya amince da tayin ne bayan matsin lamba daga wasu manyan ‘yan siyasa masu tasiri daga yankunan Arewa maso Yamma da Kudu maso Kudu.
Majiyar ta ce Atiku ya bai wa Amaechi tabbacin cewa zai taka muhimmiyar rawa a lokacin yakin neman zabe da kuma idan suka kafa gwamnati.
Amaechi ba sabon shiga ba ne a harkokin yakin neman zabe, domin ya taba zama Darakta Janar na kungiyar yakin neman zaben jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a lokacin mulkin marigayi Shugaba Muhammadu Buhari.
A wani bangaren kuma, jigo a jam’iyyar ADC, Eze Chukwuemeka Eze, ya musanta ikirarin da Dele Momodu ya yi cewa Amaechi ya ki amincewa da mukamin mataimakin shugaban kasa.
Eze ya bayyana a cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Alhamis cewa kalaman Momodu ra’ayi ne na kansa da ka iya haifar da rashin jituwa da tashin hankali a cikin jam’iyyar.
Ya ce abin da Amaechi ya fada a baya kawai yana nuna cewa a lokacin ba a yi masa tayin mukamin a hukumance ba.
Masu sa ido kan harkokin siyasa na ganin cewa zaben Amaechi da Atiku ya yi wata dabara ce ta siyasa domin fuskantar tikitin Peter Obi da Rabiu Musa Kwankwaso na jam’iyyar Nigeria Democratic Congress (NDC) a zaben shugaban kasa da za a gudanar ranar 16 ga Janairun 2027.
