Wani sabon rahoto na GSMA Mobile Economy Africa 2025 ya bayyana cewa fannin sadarwa ya bayar da gudunmawar dala biliyan 220 ga tattalin arzikin Afirka a shekarar 2024, wanda ya kai kashi 7.7 cikin ɗari na jimillar GDP na nahiyar.
Da yake jawabi a wani taron manufofin sadarwa da aka gudanar a Kinshasa, wanda Shugaban Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Kongo, Félix Tshisekedi ya halarta, Babban Jami’in Harkokin Dokoki na kamfanin Airtel Africa, Daddy Mukadi, ya bukaci gwamnatocin Afirka da su ɗauki fannin sadarwa a matsayin ginshiƙin tattalin arziki, ba kawai a matsayin fannin tallafi ba.
Mukadi ya ce, “Ba za a ƙara kallon fannin sadarwa a matsayin wani bangare na tallafi kawai ba. Yanzu ya zama muhimmin fanni na tattalin arziki.”
Mukadi, wanda kuma shi ne shugaban Ƙungiyar Manufofin Afirka ta GSMA, ya bayyana cewa kusan dukkan fannoni da suka haɗa da tsaro, harkokin kuɗi, sufuri da lafiya suna dogaro da fasahar zamani domin samun ci gaba.
Rahoton ya nuna cewa duk da cewa hanyoyin sadarwar wayar salula sun mamaye kusan kashi 95 cikin ɗari na al’ummar Afirka, har yanzu kusan kashi 75 cikin ɗari na jama’a ba sa amfani da intanet. An bayyana tsadar wayoyin hannu a matsayin babban ƙalubalen da ke hana mutane shiga duniyar fasahar zamani.
Mukadi ya ba da shawarar a dakatar da harajin shigo da kayayyaki da sauran haraji na tsawon shekaru biyu zuwa uku kan wayoyin hannu masu araha da farashinsu ke tsakanin dala 40 zuwa 150, domin rage farashin su da kuma ƙara yawan masu amfani da intanet.
Haka kuma, ya yi kira da a soke harajin shigo da kayan aikin sadarwa na tsawon shekaru uku domin taimakawa wajen faɗaɗa hanyoyin sadarwa da inganta isar da sabis a yankunan da ba su da wadataccen tsarin sadarwa.
GSMA ta yi hasashen cewa gudunmawar fannin sadarwa ga tattalin arzikin Afirka za ta ƙaru zuwa dala biliyan 270 nan da shekarar 2030, amma hakan zai yiwu ne kawai idan gwamnatoci suka aiwatar da manufofin da za su ƙarfafa zuba jari, rage kuɗaɗen gudanarwa da kuma faɗaɗa damar samun sabis na sadarwa.
A ƙarshe, Mukadi ya jaddada cewa ɗaukar fannin sadarwa a matsayin ginshiƙin ci gaba zai taimaka wajen hanzarta sauyin fasahar zamani a Afirka, samar da ayyukan yi da kuma ƙarfafa tattalin arzikin nahiyar wajen fuskantar ƙalubale na gaba.
