Trends

Majalisar Wakilai Ta Amince da Kudirin Kafa ’Yan Sandan Jihohi

Majalisar Wakilai ta Tarayya ta amince da kudirin gyaran kundin tsarin mulki da ke neman kafa tsarin ’yan sandan jihohi a faɗin Najeriya.

’Yan majalisar sun amince da kudirin ne a zaman majalisar na ranar Alhamis bayan gudanar da ƙuri’a kan gyaran kundin tsarin mulkin da aka gabatar.

Amincewar da majalisar ta yi da kudirin na ɗaya daga cikin manyan matakai a muhawarar da aka shafe shekaru ana yi kan raba ikon aikin ’yan sanda daga gwamnatin tarayya zuwa jihohi, tare da bai wa jihohi damar kafa da gudanar da rundunonin ’yan sandansu bisa doka.

Wannan ci gaba na zuwa ne a daidai lokacin da ake ci gaba da kira ga gwamnati da ta yi gyare-gyaren tsaro domin ƙarfafa yaƙi da laifuffuka da sauran matsalolin tsaro a sassa daban-daban na ƙasar.

Masu goyon bayan kudirin na ganin cewa kafa ’yan sandan jihohi zai taimaka wajen inganta tsaro saboda jami’an za su fi sanin yankunansu da matsalolin da ke cikinsu. Sai dai wasu na nuna damuwa kan yiwuwar amfani da rundunonin wajen manufofin siyasa idan ba a samar da isassun matakan kariya ba.

Ana sa ran ƙarin bayani kan tanade-tanaden kudirin da sakamakon ƙuri’ar da aka kaɗa zai fito yayin da ake ci gaba da tattaunawa kan batun.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *