Asusun Ba da Lamuni na Duniya (IMF) ya yi hasashen cewa bashin waje na Najeriya zai ƙaru daga dala biliyan 51.9 a shekarar 2025 zuwa dala biliyan 72.6 a shekarar 2027.
Rahoton IMF na 2026 Article IV Consultation ya nuna cewa wannan na nufin ƙarin kusan kashi 39.9 cikin ɗari cikin shekaru biyu, lamarin da ke haifar da damuwa kan yadda Najeriya za ta ci gaba da ɗaukar nauyin bashin ta.
IMF ta yi gargadin cewa matsin lambar kashe kuɗi a lokacin zaɓe, tare da talauci da ƙarancin abinci, na iya ƙara gibin kasafin kuɗi da kuma buƙatar ƙarin bashi.
Ta ce: “Matsin lambar kashe kuɗi daga tsananin talauci da ƙarancin abinci, ciki har da lokacin shirin zaɓe, na iya faɗaɗa gibin kasafin kuɗi da ƙara buƙatar kuɗin cike giɓi.”
Rahoton ya nuna cewa jimillar bashin waje, ciki har da na kamfanoni masu zaman kansu, zai ƙaru daga dala biliyan 109.3 a 2025 zuwa dala biliyan 132 a 2027, yayin da nauyin biyan bashi ke ƙara tsananta.
Haka kuma, biyan riba kan bashin gwamnati zai tashi daga dala biliyan 2 a 2025 zuwa dala biliyan 3 a 2027. IMF ta ce fiye da kashi 53.2 cikin ɗari na kuɗaɗen shigar gwamnatin tarayya a 2025 an kashe su kan biyan riba, kuma ana sa ran hakan zai ci gaba har zuwa 2027.
Rahoton ya kuma nuna damuwa kan shirin Najeriya na tara dala biliyan 5 ta hanyar Total Return Swap (TRS) tare da First Abu Dhabi Bank. Wakilin IMF a Najeriya, Christian Ebeke, ya bayyana cewa irin wannan tsarin na iya zama mai “ɓoye gaskiya” kuma yana iya jefa ƙasar cikin haɗarin ƙarin biyan kuɗi idan darajar Naira ta ragu.
Duk da ƙarin bashin, IMF ta ce haɗarin tabarbarewar tattalin arzikin Najeriya yana cikin matsakaici, saboda ingantuwar haɓakar tattalin arziki, ƙarin ƙimar Naira, da kuma gyare-gyaren da aka yi a baya.
Ta ce an rage yawan bashin da ya danganci GDP daga kashi 39.3 a 2024 zuwa kashi 36.1 a 2025.
Asusun ya yi hasashen cewa tattalin arzikin Najeriya zai ƙaru da kashi 4.1 a 2026 da kuma kashi 4.3 a 2027, duk da cewa hauhawar farashi sakamakon rikice-rikicen duniya na iya shafar rayuwar jama’a.
IMF ta kuma shawarci gwamnati da ta ƙara faɗaɗa shirye-shiryen tallafin kuɗi ga talakawa, tare da ci gaba da gyare-gyare a fannin ababen more rayuwa, wutar lantarki, noma, da kiwon lafiya.
