Hukumar Kula da Wutar Lantarki ta Najeriya (NERC) ta bayyana cewa kamfanonin rarraba wutar lantarki (DisCos) sun yi asarar kusan Naira biliyan 310 a rubu’in farko na shekarar 2026, sakamakon wutar da ba a lissafa ba da kuma raunin karɓar kuɗin wuta.
Rahoton ya nuna cewa DisCos sun karɓi wutar da darajarta ta kai Naira biliyan 907 a wannan lokaci, amma sun lissafa wutar da darajarta ta kai Naira biliyan 757 kacal, yayin da suka karɓi Naira biliyan 598, wanda ya bar Naira biliyan 150 ba a lissafa ba da kuma Naira biliyan 159 ba a karɓa ba.
A watan Janairu, an ba DisCos wutar da darajarta ta kai Naira biliyan 336, amma sun lissafa Naira biliyan 268, kuma sun karɓi Naira biliyan 205 kacal. Hakan ya bar Naira biliyan 68 ba a lissafa ba da kuma Naira biliyan 63 da ba a biya ba. Ingancin lissafin wuta ya tsaya a kashi 79.7%, yayin da ingancin karɓar kuɗi ya kai kashi 76.3%.
A watan Fabrairu, an samu ɗan ci gaba, inda ingancin lissafi ya tashi zuwa kashi 87.4% sannan ingancin karɓar kuɗi ya kai kashi 81.2%. DisCos sun lissafa Naira biliyan 242 daga cikin Naira biliyan 277 da aka ba su, kuma sun karɓi Naira biliyan 197, sai dai Naira biliyan 46 ba a biya ba.
A watan Maris, DisCos sun karɓi wutar da darajarta ta kai Naira biliyan 294, sun lissafa Naira biliyan 246, sannan sun karɓi Naira biliyan 196, inda Naira biliyan 47 ba a lissafa ba da kuma Naira biliyan 50 ba a biya ba. Jimillar ingancin dawo da kuɗi ya kai kashi 81%.
Rahoton ya nuna cewa akwai bambanci sosai tsakanin kamfanonin. Eko Electricity Distribution Company da Ikeja Electricity Distribution Company sun nuna kyakkyawan aiki, inda Eko DisCo har ma ya wuce kashi 100% na karɓar kuɗi a watan Fabrairu sakamakon tattara basussuka.
Sai dai Kaduna Electricity Distribution Company ta yi ƙasa ƙwarai, inda ta samu kashi 41% na dawo da kuɗi, yayin da Jos da Yola DisCos suma suka kasance cikin mafi raunin masu aiki.
NERC ta ce matsalolin sun haɗa da ƙarancin na’urorin awo (meter), satar wuta, yin bypass na mita, raunin aiwatar da doka, da kuma rashin ingantaccen tsarin karɓar kuɗi, wanda ke ci gaba da lalata tsarin kuɗin ɓangaren wutar lantarki.
Haka kuma, Hukumar Tsarin Wutar Lantarki Mai Zaman Kanta ta Kasa (NISO) ta bayyana cewa an samu manyan satar wuta a layin wuta na Ikorodu-Sagamu, inda aka yi asarar kusan megawatt 180, adadin da ya yi daidai da rabon wutar yau da kullum na Jos DisCo. NISO ta yi gargadin cewa irin wannan satar wuta na iya lalata daidaiton grid ɗin wutar lantarki da kuma rage kuɗaɗen shiga a ɓangaren.
