Trends

Cutar Corona: Jami’ar Cambridge ta Gwada Allurar Rigakafin na Farko Kirkirar AI

Masana kimiyya a Jami’ar Cambridge tare da kamfanin binciken fasahar kere-kere na DIOSynVax sun kammala gwajin farko a kan mutane na wata sabuwar allurar rigakafi da aka kirkira ta amfani da fasahar basirar na’ura (AI), wadda aka tsara domin kare mutane daga nau’o’in cututtukan coronavirus daban-daban.

Gwajin na farko ya hada da lafiyayyun mutane 39, kuma sakamakon ya nuna cewa allurar na da aminci tare da rashin haifar da wata babbar illa ga wadanda aka yi wa gwajin.

Masu binciken sun bayyana cewa allurar tana kai hari ga dangin kwayoyin cutar Sarbecovirus, wadanda suka hada da COVID-19, SARS da wasu kwayoyin cuta makamantansu da ake samu a jemagu, wadanda ka iya yaduwa zuwa mutane a nan gaba.

Farfesa Jonathan Heeney, wanda ya jagoranci binciken, ya ce sabuwar fasahar ta sauya tsarin samar da allurar rigakafi daga mayar da martani bayan barkewar cuta zuwa shirin kariya tun kafin barkewar annoba.

Ya ce, “Mun samar da wata hanya da za ta ba da kariya daga kwayoyin cuta ko da suna ci gaba da sauyawa zuwa sabbin nau’o’i.”

Ba kamar alluran rigakafi na gargajiya da ake sabunta su ga kowace sabuwar nau’in cuta ba, sabuwar allurar ta AI tana amfani da abin da masana suka kira “super-antigen”, wanda aka gina daga siffofin kwayoyin halitta da suka yi kama a tsakanin nau’o’in kwayoyin cuta da dama.

Wannan hanya na koyar da garkuwar jiki yadda za ta gane da kuma yakar nau’o’in cutar da ake da su yanzu da kuma wadanda ka iya bayyana a nan gaba.

An gudanar da gwajin allurar ne a biranen Southampton da Cambridge ta hanyar amfani da wata na’ura mai harba magani ba tare da amfani da allura ba.

Sakamakon farko ya nuna cewa allurar ta haifar da martanin garkuwar jiki ba kawai ga sanannun kwayoyin coronavirus ba, har ma da wasu kwayoyin cuta da ake samu a dabbobi wadanda har yanzu ba su haddasa barkewar cuta a cikin mutane ba.

Babban mai binciken gwajin, Farfesa Saul Faust, ya ce idan aka samu ci gaba wajen samar da irin wadannan allurai kafin barkewar wata sabuwar annoba, za a iya ceton rayukan miliyoyin mutane, kauce wa killace jama’a da kuma kare tattalin arziki daga mummunar illa.

Masana sun yi imanin cewa za a iya amfani da wannan fasaha wajen samar da kariya daga wasu hadaddun cututtuka kamar mura mai tsanani (influenza) da Ebola, wanda zai taimaka wajen tunkarar annobobi a nan gaba.

Sai dai masu binciken sun yi gargadin cewa har yanzu akwai bukatar gudanar da manyan gwaje-gwajen mataki na biyu (Phase 2) domin tabbatar da inganci da tasirin allurar a tsakanin mutane masu bambancin shekaru da yanayi.

An fi samun tallafin aikin ne daga shirin Innovate UK, kuma ana kallon wannan a matsayin daya daga cikin gwaje-gwajen farko a duniya da aka yi wa allurar rigakafi da aka kirkira ta amfani da basirar na’ura (AI) a kan mutane.