Kamfanonin rarraba wutar lantarki na Najeriya (DisCos) sun tara kimanin Naira biliyan 597.55 daga hannun masu amfani da wutar lantarki a rubu’in farko na shekarar 2026, a cewar Hukumar Kula da Wutar Lantarki ta Najeriya, wato Nigerian Electricity Regulatory Commission, duk da ci gaba da fama da katsewar wuta da sauran matsalolin da ke addabar fannin.
Rahoton ya nuna cewa DisCos sun tara Naira biliyan 204.74 a watan Janairu, Naira biliyan 196.68 a watan Fabrairu, da kuma Naira biliyan 196.13 a watan Maris, wanda ya kai matsakaicin kusan Naira biliyan 199 a kowane wata.
A watan Janairu, kamfanonin sun aika takardun kuɗin wuta da suka kai Naira biliyan 268.20, amma sun samu damar karɓar Naira biliyan 204.74 kacal, lamarin da ya bar Naira biliyan 63.46 ba a karɓa ba. Ingancin fitar da takardun kuɗi ya kai kashi 79.72 cikin 100, yayin da ingancin karɓar kuɗaɗen ya tsaya a kashi 76.34 cikin 100.
A watan Fabrairu kuwa, an fitar da takardun kuɗi da suka kai Naira biliyan 242.29, inda aka karɓi Naira biliyan 196.68. Hakan ya bar Naira biliyan 45.61 da ba a karɓa ba. Ingancin fitar da takardun kuɗi ya ƙaru zuwa kashi 87.44 cikin 100, yayin da ingancin karɓar kuɗaɗen ya kai kashi 81.17 cikin 100.
A watan Maris, DisCos sun aika takardun kuɗi na Naira biliyan 246.43, amma sun karɓi Naira biliyan 196.13 kawai, wanda ya bar Naira biliyan 50.30 ba a karɓa ba. Ingancin fitar da takardun kuɗi ya kasance kashi 83.89 cikin 100, yayin da ingancin karɓar kuɗaɗen ya tsaya a kashi 79.59 cikin 100.
Rahoton ya nuna cewa akwai bambanci a yadda kamfanonin rarraba wutar lantarki 11 ke gudanar da ayyukansu. Kamfanonin Eko Electricity Distribution Company da Ikeja Electric sun kasance cikin mafi ƙwarewa, inda Eko DisCo ta samu nasarar karɓar kuɗaɗen da suka haura kashi 100 cikin 100 na abin da aka biya a watan Fabrairu.
Sai dai kuma kamfanonin Kaduna Electricity Distribution Company da Jos Electricity Distribution Company sun kasance cikin waɗanda suka fi fuskantar matsaloli, inda Kaduna DisCo ta samu ingancin karɓar kuɗi na kashi 41.20 cikin 100 kacal.
Masu amfani da wutar lantarki sun ci gaba da nuna damuwa kan tsadar kuɗin wuta duk da yawan katsewar da ake samu sakamakon ƙarancin iskar gas da ake amfani da ita wajen samar da lantarki.
Yawan wutar da ake samarwa a ƙasa ya ragu daga kusan megawatt 4,000 zuwa ƙasa da megawatt 2,000, lamarin da ya tilasta wa Transmission Company of Nigeria rage yawan wutar da ake rabawa zuwa sassa daban-daban na ƙasar.
Ya zuwa ranar 23 ga Fabrairu, 2026, yawan iskar gas da ake samarwa ya kai miliyan 692 na cubic feet a rana (mmscf/day), wanda bai kai kashi 43 cikin 100 na buƙatar miliyan 1,629 na cubic feet a rana da ake buƙata domin samar da isasshen wutar lantarki ba.
Masu ruwa da tsaki a fannin sun buƙaci a ƙara inganta tsarin saka mitoci, a tsaurara matakan yaƙi da satar wutar lantarki, tare da inganta hulɗa da kwastomomi domin ƙara yawan kuɗaɗen da ake tarawa. Sun kuma yi gargaɗin cewa ƙarancin ababen more rayuwa da matsalolin ƙarancin kuɗaɗe na ci gaba da barazana ga dorewar fannin wutar lantarki a Najeriya.
