Trends

CBN Ta Fitar da Sabon Kundin Dokokin Musayar Kuɗaɗen Waje

Yemi Cardoso Shugaban babban Bankin Najeriya wato CBN

Babban Bankin Najeriya (CBN) ya fitar da bugu na huɗu na Kundin Dokokin Musayar Kuɗaɗen Waje (Foreign Exchange Manual), da nufin daidaita kasuwar canjin kuɗi ta hanyar ƙarfafa bayyana gaskiya, tsaurara bin ƙa’idoji da kuma fayyace dokokin gudanar da harkokin musayar kuɗi.

Gwamnan CBN, Olayemi Cardoso, ya bayyana cewa musayar kuɗaɗen waje ba kawai wata hanyar gudanar da harkokin kuɗi ba ce, illa muhimmiyar hanya ce da ke tallafa wa tattalin arzikin ƙasa. Ya ce tana taimakawa wajen tabbatar da daidaiton farashi, sauƙaƙa zirga-zirgar kayayyaki da jari, tare da tasiri kan amincewar masu zuba jari.

Sabon kundin, wanda ya fara aiki daga ranar 1 ga Yuni, 2026, ya maye gurbin wanda aka fitar a shekarar 2018. CBN ya ce an yi wannan gyara ne domin dacewa da sabbin sauye-sauyen da suka faru a cikin gida da kuma duniya, ciki har da sauyin farashin mai, ƙarancin kuɗaɗen waje da kuma sauye-sauyen da ake yi domin samar da tsarin musayar kuɗi na kasuwa.

Mataimakin Gwamnan CBN, Muhammad Abdullahi, ya ce sake duba kundin wani ɓangare ne na manyan gyare-gyaren da bankin ke aiwatarwa domin dawo da amincewa, ƙara bayyana gaskiya, bunƙasa wadatar kuɗaɗen musayar waje da kuma inganta yadda kasuwar ke aiki. Ya jaddada cewa kasuwar musayar kuɗi ta zamani ba za ta bunƙasa ba idan tana fama da rashin bayyana gaskiya, rarrabuwar tsarin aiki, jinkiri da kuma cikas marasa amfani.

Daga cikin muhimman sauye-sauyen da aka yi akwai daidaita tsarin Personal Travel Allowance (PTA) da Business Travel Allowance (BTA) da ƙa’idojin masu canjin kuɗi (Bureau de Change), inda aka tanadi cewa kashi 75 cikin 100 na mu’amaloli za a riƙa gudanar da su ta hanyar lantarki.

Haka kuma, an ƙara yawan kuɗin da ake iya biya a gaba wajen shigo da kaya daga kashi 15 zuwa kashi 30 cikin 100, yayin da aka cire kuɗin cike takardar Form NXP da ake amfani da ita wajen fitar da kaya zuwa ƙasashen waje.

Sauran sabbin tanade-tanaden sun haɗa da bai wa ɗalibai damar biyan kuɗin makaranta a ƙasashen waje har zuwa dala 25,000 a kowace zangon karatu, ƙirƙirar asusun zuba jari ga waɗanda ba mazauna Najeriya ba, da kuma cire wajabcin amfani da Form A wajen aika kuɗi ta asusun domiciliary, domin rage cikas na gudanarwa.

Shugabannin manyan bankuna sun yi maraba da sabon kundin. Shugaban UBA, Oliver Alawuba, ya ce kundin zai ƙarfafa bayyana gaskiya da bin ƙa’ida a kasuwar musayar kuɗi. Shi ma Shugaban Access Holdings, Roosevelt Ogbonna, ya bayyana cewa sabbin dokokin za su kawar da ruɗani tare da ƙara amincewa da kasuwar.

Jami’an Ma’aikatar Kuɗi sun bayyana kundin a matsayin wani ɓangare na manyan gyare-gyaren tattalin arzikin Najeriya, amma sun jaddada cewa nasarar sa za ta dogara ne da yadda za a tabbatar da aiwatar da dokokin yadda ya kamata.

A ƙarshe, Cardoso ya ce nasarar aiwatar da wannan kundi za ta dogara ne da haɗin kai da jajircewar dukkan masu ruwa da tsaki a harkar musayar kuɗaɗen waje.