Duk da matatar mai ta Dangote ta rage farashin man jirgin sama (Jet A1) zuwa ₦1,650 kan kowace lita, farashin mai ya ci gaba da zama tsakanin ₦1,900 zuwa ₦2,000 a sassa daban-daban na Najeriya, binciken jaridar Daily Trust ya nuna.
Matatar ta sanar da rage farashin ne a ranar Litinin, tare da gabatar da tsarin bashi mara riba na kwanaki 30 da banki ke lamunta, da kuma sauya tsarin biyan kuɗi daga dalar Amurka zuwa naira, domin rage wa kamfanonin jiragen sama nauyin kashe kuɗi.
Sai dai duk da wannan mataki, farashin siyarwa a kasuwa bai sauya ba. A Abuja da Kano, Jet A1 ana sayar da shi a kusan ₦2,000 kan kowace lita, yayin da a Lagos farashin yake tsakanin ₦1,910 zuwa ₦1,925. Wasu dillalai ma sun aika wa kamfanonin jiragen sama takardun sanar da yiwuwar ƙarin sauye-sauyen farashi.
Wani dillali ya bayyana cewa sauyin farashin na da nasaba da “ci gaba da rashin daidaito a kasuwar man fetur, musamman tashin farashin sayen mai daga depot da kuma ƙarin kuɗaɗen jigila a sarkar rarrabawa.”
Hukumar NMDPRA ta sanya farashin man jirgi a Abuja zuwa ₦2,037 kan lita, yayin da a Lagos ta kayyade shi tsakanin ₦1,760 zuwa ₦1,988. Duk da haka, ‘yan kasuwa sun ce har yanzu bambancin farashi na ci gaba.
Wani jami’in kamfanin jirgin sama ya ce: “Sanarwar Dangote ta ba mu fata, amma abin da muke gani a kasuwa ya bambanta. Yawancin dillalai har yanzu ba su sauya farashi ba.”
Tsadar man jirgi ta riga ta tilasta wasu kamfanonin jiragen sama rage yawan zirga-zirgar jirage, yayin da wasu ke gargadin yiwuwar rage hanyoyin zirga-zirga ko ƙara farashin tikiti.
Rahotanni sun nuna cewa matsalar ta ƙara tsananta sakamakon rikicin Amurka da Isra’ila da Iran da kuma rufe mashigar Strait of Hormuz, wadda ke ɗauke da kusan kashi ɗaya cikin biyar na mai da ake fitarwa a duniya.
Masana sun bayyana cewa duk da matakin Dangote na rage farashi da ake ganin zai ƙara gasa a kasuwa, abubuwa kamar jigila, sauyin farashin dala, haraji, kuɗin ajiya da kuma tsohon mai da aka siya da tsada suna hana sauyin farashi a kasuwa nan take.
Wani masanin harkokin sufurin jiragen sama, Kyaftin Samuel Caulcrick, ya yi kira ga hukumar FCCPC da ta binciki ribar da dillalan ke samu.
Ya ce: “Idan farashin fitowa daga matatar yana ₦1,650, abin da ya kamata ya rage shi ne ribar dillalai da kuɗin jigila kawai. FCCPC ya kamata ya tabbatar da gaskiya domin hana cin zarafin masu amfani da kaya.”

