Rikicin Gabas ta Tsakiya: Farashin Danyen Man Najeriya Ya Kusanci Dala 120

Farashin danyen man Bonny Light, wanda shi ne babban nau’in man fetur na Najeriya, ya kai kusan dala 117 kan kowace ganga, yayin da yake kara kusantar dala 120 sakamakon ci gaba da rikicin da ke tsakanin Amurka da Iran wanda ya girgiza kasuwannin mai na duniya.

Bayanan da Central Bank of Nigeria ta fitar sun nuna cewa farashin man na kara komawa matakan da aka samu a watan Afrilu, lokacin da danyen man Najeriya ya kusa kai dala 140 kan kowace ganga. A mafi yawan lokuta, danyen man Najeriya kan fi farashin Brent, wanda ake amfani da shi a matsayin ma’aunin farashin mai a duniya.

Farashin mai ya tashi daga kusan dala 70 kan kowace ganga tun bayan barkewar yakin, musamman bayan rufe mashigar ruwa ta Strait of Hormuz, wadda ke daukar kusan kashi 20 cikin 100 na jigilar man duniya.

Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen Iran, Esmaeil Baghaei, ya tabbatar da cewa Tehran ta aika da sabon martaninta ga shawarwarin Amurka ta hannun Pakistan, wadda ke shiga tsakani a tattaunawar.

Ya ce bukatun Iran sun hada da sakin kadarorin kasar da aka daskarar da su da kuma dage takunkumin tattalin arziki da aka kakaba mata.

“Batutuwan da aka gabatar bukatu ne na Iran da tawagar masu tattaunawa ta kasar ta tsaya kai da fata wajen karewa a duk zagayen tattaunawa,” in ji shi.

Iran ta kuma bukaci a biya ta diyya kan barnar yakin, a kawo karshen killacewar jiragen ruwan Amurka da kuma dakatar da fada a dukkan bangarori, ciki har da kasar Lebanon inda sojojin Isra’ila ke ci gaba da kai hare-hare duk da yarjejeniyar tsagaita wuta.

A gefe guda, Shugaban Amurka, Donald Trump, ya gargadi Iran ta shafinsa na Truth Social cewa: “Lokaci na kurewa… Gara su yi gaggawa, ko kuma babu abin da zai rage musu. Lokaci yana da muhimmanci!”

Trump ya bayyana yarjejeniyar tsagaita wutar a matsayin wadda “ke dab da rushewa.”

Rahotanni daga kamfanin dillancin labarai na Fars News Agency sun ce shirin sulhu mai maki biyar da Amurka ta gabatar ya bukaci Iran ta ci gaba da rike cibiyar nukiliyarta guda daya kacal tare da mika ajiyar sinadarin uranium da ta tace ga Amurka. Sai dai Tehran ta yi watsi da tayin, tana mai dagewa kan ci gaba da iko da mashigar Strait of Hormuz.

A halin yanzu kuma, Sakataren Baitul Malin Amurka, Scott Bessent, ya ce zai bukaci ministocin kudin kungiyar kasashen G7 su mara wa takunkumin Amurka baya domin dakile abin da ya kira “na’urar yakin Iran.”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *