Tsohon Gwamnan Jihar Kogi, Yahaya Bello, ya lashe zaben fidda gwani na jam’iyyar APC domin takarar kujerar Sanata a Mazabar Kogi Ta Tsakiya.
An bayyana sakamakon ne a ranar Litinin ta hannun jami’in da ke sanar da sakamakon, Dr Sadiq Mohammed, wanda ya ce Yahaya Bello ya samu jimillar kuri’u 72,349, inda ya doke abokan takararsa, Ibrahim Yakubu Adoke wanda ya samu kuri’u 315, da kuma Momoh Yusuf Obaro wanda ya samu kuri’u 188.
Bisa sakamakon da aka tattara daga kananan hukumomi biyar na mazabar, Bello ya samu kuri’u kamar haka: Adavi 18,341; Ajaokuta 10,298; Ogori 5,146; Okehi 8,943; da Okene 29,621.
A bangaren Kogi Ta Yamma kuwa, rahotanni sun nuna cewa Sanata mai ci, Sunday Karimi, na kan gaba a zaben fidda gwani yayin da ake ci gaba da tattara sakamako.
Wannan ya biyo bayan janyewar wasu manyan ‘yan takara, ciki har da Sanata Smart Adeyemi da Samuel Bamidele Aro da wasu da dama kafin kammala zaben, lamarin da ya sa aka ce Sanatan na matukar kusantar nasara.
A Kogi Ta Gabas kuma, rahotanni sun nuna cewa Sanata mai ci, Jibrin Isah Echocho, na fuskantar kalubale a zaben fidda gwani da ke gudana, inda aka ce ya sha kaye a mazabar Dekina da kuri’u biyu kacal, yayin da abokin takararsa, Dr Joe Erico Ameh, ya samu kuri’u 19,805.
Rahotanni sun bayyana Dr Joe Erico a matsayin wanda manyan masu ruwa da tsaki a jihar ke mara wa baya.
Wasu manyan ‘yan takara, ciki har da Murtala Ajaka da Jibrin Echocho, sun koka kan yadda aka gudanar da zaben fidda gwani, suna masu cewa ba a bi ƙa’idojin jam’iyya yadda ya kamata ba.
