Jam’iyyar APC ta yi karin haske kan sakamako masu karo da juna na zaben fid-da-gwani na dan takarar Majalisar Tarayya mai wakiltar Pankshin/Kanke/Kanam da ke Jihar Filato.
Shugaban Kwamitin Zaben ya bayyana cewa daya ta bayayana cewa daya sakamakon na bogi ne, tana mai kira ga jama’a da su yi watsi da shi, tare da cewa sakamakon da baturen zaben ya tabbatar ne sahihi.
Wannan ya faru ne bayan bullar sakamako biyu masu karo da juna, inda a daya, aka tabbatar dan majalisa mai ci, Yusuf Gadgi, a matsayin wanda ya yi nasara, a yaiyn da daya kuma aka bayyana Dakta John Tongshinen a matsayin wanda ya yi nasara.
A ranar Lahadi ne baturen zaben fid-da-gwanin, Barista Nandom Andrew Kura, ya sanar cewa Hon. Yusuf Adamu Gagdi ya yi nasarar zama dan takarar APC na Mazabar Pankshin/Kanke/Kanam ta tarayya da kuri’u 29,207.
Andrew Kura ya sanar cewa, “Mutum biyar ne suka fafata, inda Adamu Yusuf Gagdi ya samu kuri’u 29, 207. Henry Goti ya samu 293, sai Zhiphion Chrysantus ma kuri’u 848 , Abbas Adamu kuri’a 430 votes a yayin da John Tongshinai ke da kuri’u 372.
“Jimillar kuri’a 31,150 aka jefa. Bisa ikon da aka ba ni na gudanar da zaben fid-da-gwani ma mazabar PKK, ina sanar da Hon. Yusuf Adamu Gagdi a matsayin wanda ya lashe wannan zaben.“
Sai dai a wani taron manema labarai da aka gudanar a Pankshin ranar Lahadi, baturen zaben, Daspan Ishaya, ya fitar da sanarwar cewa Dakta John Tongshinen na ya samu mafi yawan kuri’u a fafatawar.
Ishaya ya bayyana cewa Tongshinen ya samu kuri’u 29,968 a fatawar, a yayin da Hon. Gagdi ya samu kuri’u 5,849 votes, sai John Pia, mai kuri’u 51.
Amma da take yin karin haske kan lamarin a sakatariyar APC ta jihar, shugaban kwamitin zaben ’yan takara na jihar, Hon. Stella Oketete, ta bayyana cewa Baturen Zaben da ta san da zamansa shi ne Nandom Andrew Kura, wanda ya sanar cewa Gagdi ya yi nasara.
“Baturen zaben dan takara na mazabar Pankshin/Kanke/Kanam shi ne Barista Nandom Andrew Kura,” in ji ta.
