Trends

Zargin Laifin Yanan Gizo: Kotu Ta Ba El-Rufai Belin Naira Miliyan 100

Mallam Nasir El-Rufai Tsohon gwamnan Kaduna

Wata Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta bayar da belin Naira miliyan 100 ga tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, kan zargin karya dokar Cybercrimes Act da kuma batun tsaron kasa.

Hukumar Department of State Services ce ke gurfanar da tsohon gwamnan a gaban kotu, bayan wani furuci da ya yi a talabijin cewa ya sa ido (wiretap) kan tattaunawar Mai Bai Wa Shugaban Kasa Shawara kan Tsaro, Nuhu Ribadu.

Yayin yanke hukunci kan bukatar beli, Mai Shari’a Joyce Abdulmalik ta gindaya tsauraran sharudda kafin a saki wanda ake tuhuma.

Kotun ta umurci cewa dole ne wanda zai tsaya masa ya kasance mazaunin unguwannin Maitama ko Asokoro a Abuja, kuma ya gabatar da ainihin takardar mallakar fili (Certificate of Occupancy) ga kotu.

Haka kuma, kotun ta ce dole ne wanda zai tsaya ya kasance ma’aikacin gwamnati a matakin aƙalla Grade Level 17, tare da gabatar da hujjar biyan albashi na watanni uku da kuma takardar tabbatarwa daga manajan banki a yankin da kotu ke aiki.

Bugu da kari, dole ne wanda zai tsaya ya rubuta takardar bayyana kadarori (affidavit of means), ya rattaba hannu kan takardar beli, sannan ya mika hoton fasfo na kwanan nan.

Kotun ta kuma umarci Nasir El-Rufai da ya mika dukkan fasfo dinsa na kasa da kasa ga kotu tare da gabatar da takardar biyan haraji (tax clearance) na watanni shida da suka gabata.

A matsayin sharadi, kotun ta ce dole ne ya rika zuwa hedikwatar Department of State Services a Abuja duk karshen wata Jumma’a da karfe 10 na safe domin sanya hannu a rajistar halarta har sai an kammala shari’ar.

Mai shari’a Abdulmalik ta gargadi cewa duk wanda ya karya sharuddan belin zai rasa belin nan take.

Kotun ta kuma umarci wanda ake tuhuma ya gabatar da takardar shaida daga shugaban Majalisar Masarautun Jihar Kaduna.

Daga bisani kotun ta dage shari’ar zuwa wani lokaci domin ci gaba da sauraron ta cikin gaggawa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *