Trends

Kananan Masana’antu: BOI Ta Samu Tallafin Dala Miliyan 200 daga AfDB

Bankin Masana’antu na Najeriya, Bank of Industry, ya samu tallafin lamuni na dala miliyan 200 daga African Development Bank domin fadada samar da dogon zangon jari ga kamfanonin Najeriya da ke muhimman bangarorin tattalin arziki.

A cewar AfDB, za a yi amfani da kudaden wajen tallafa wa bangarorin ababen more rayuwa, sufuri, sarrafa kayan abinci na noma, lafiya, magunguna da kuma masana’antun da ke amfani da hanyoyin kare muhalli.

Bankin ya bayyana cewa akalla kashi 30 cikin 100 na kudaden za a ware su ne domin kananan da matsakaitan masana’antu (SMEs), musamman wadanda mata da matasa ke jagoranta.

Tallafin ya kuma hada da kyautar dala 650,000 domin horaswa da karfafa wa kananan masana’antu gwiwa, inganta tsarin kula da muhalli da gudanarwa, tare da tallafa wa shirye-shiryen da ke da alaka da sauyin yanayi.

Har ila yau, wani bangare na shirin mai suna Affirmative Finance Action for Women in Africa zai taimaka wajen kara bai wa mata ‘yan kasuwa damar samun jari da kasuwanni.

Daraktan AfDB na Najeriya, Abdul Kamara, ya ce Najeriya na bukatar jari mai dorewa na dogon lokaci domin bunkasa masana’antu fiye da yadda tsarin kasuwa ke samarwa a yanzu.

Ya ce, “Wannan amincewa za ta tabbatar da cewa an karkatar da jari zuwa bangarorin da suka fi muhimmanci, musamman domin tallafa wa kananan masana’antu, mata ‘yan kasuwa da matasa masu harkokin kasuwanci.”

Shi ma Daraktan bunkasa bangaren hada-hadar kudi na AfDB, Ahmed Rashad Attout, ya bayyana cewa tallafin zai kara wa BOI karfin samar da rance mai saukin sharadi ga bangarori masu tasiri a tattalin arziki.

Manajan Daraktan BOI, Olasupo Olusi, ya yi maraba da hadin gwiwar, yana mai bayyana cewa bankin ya riga ya kammala biyan wani tsohon bashin dala miliyan 100 da AfDB ta bayar a shekarar 2025.

A cewarsa, “Wannan tallafi ba wai kawai batun samar da kudade ba ne, yana da nasaba da bunkasa masana’antu, karfafa kasuwancin mata da matasa, habaka masana’antun cikin gida da kuma taimakawa Najeriya wajen gina tattalin arziki mai juriya.”

Ana sa ran shirin zai taimaka wajen samar da ayyukan yi, kara kudaden shiga daga haraji, bunkasa fitar da kayayyaki zuwa kasashen waje da rage kashe kudaden musayar kasashen waje ta hanyar maye gurbin kayayyakin da ake shigowa da su daga waje.

Shirin ya yi daidai da dabarun shekaru 10 na African Development Bank na bunkasa tattalin arziki mai dorewa da kare muhalli, tare da mayar da hankali wajen samar da jari, karfafa mata da matasa, da gina masana’antu da ababen more rayuwa masu juriya a Najeriya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *