World Health Organization (WHO) ta tabbatar wa jama’a cewa hadarin da ke tattare da barkewar cutar hantavirus da aka samu kwanan nan har yanzu yana da matukar ƙanƙanta, duk da shirye-shiryen da kasashe ke yi na dawo da fasinjojin jirgin ruwa mai suna MV Hondius da abin ya shafa.
Mutane uku ne suka mutu a yayin tafiyar jirgin, ciki har da ma’aurata ‘yan ƙasar Holland da wata mata ‘yar ƙasar Jamus. Sai dai jami’an WHO sun jaddada cewa cutar ba ta da saurin yaduwa sosai tsakanin mutane.
Mai magana da yawun WHO, Christian Lindmeier, ya ce: “Wannan cuta tana da haɗari ga wanda ya kamu da ita kai tsaye, amma haɗarin ga sauran jama’a yana da matuƙar ƙasa.”
Rahotanni sun nuna cewa barkewar cutar ta shafi kwayar cutar Andes, wadda ita ce kaɗai daga cikin hantavirus da aka tabbatar tana iya yaduwa daga mutum zuwa mutum, lamarin da ya haifar da fargaba a farko.
Sai dai Lindmeier ya bayyana cewa har ma wasu fasinjojin da suke zama a ɗaki guda ba dukkansu suka kamu da cutar ba, abin da ke nuna cewa yaduwar cutar tsakanin mutane tana da iyaka sosai.
WHO ta tabbatar da samun mutane biyar da suka kamu da cutar a hukumance tare da wasu uku da ake zargi, amma ta ce a halin yanzu babu wani mai ɗauke da cutar da ya rage a cikin jirgin.
Ana sa ran jirgin, wanda ke ɗauke da kusan mutane 150, zai tsaya a gabar Tenerife ranar Lahadi, inda za a kwashe fasinjojin zuwa kasashensu karkashin tsauraran matakan kariya daga kamuwa da cuta.
WHO ta kuma bayyana cewa wani ma’aikacin jirgin sama na kamfanin KLM da ya yi hulɗa da wani fasinja mai ɗauke da cutar daga baya ya gwada lafiya ba tare da ya kamu ba, abin da hukumar ta bayyana a matsayin “labari mai kyau,” yana nuna cewa hantavirus ba ta yaduwa kamar COVID-19.
Fasinjojin da ke cikin jirgin sun bayyana cewa hankalinsu kwance yake, yayin da ake amfani da takunkumin fuska da kiyaye tazara a tsakaninsu.
Wani mai wallafa bidiyo a shafin YouTube, Kasem Ibn Hattuta, wanda ke cikin jirgin, ya ce: “Kowa yana cikin kwanciyar hankali, mutane suna murmushi tare da daukar lamarin cikin nutsuwa.”
Kasashen United Kingdom da Spain sun sanar da shirinsu na dawo da ‘yan kasarsu, yayin da ake binciken wasu da ake zargi da kamuwa da cutar a yankunan Birtaniya masu nisa kamar Tristan da Cunha.
WHO ta sake jaddada cewa cutar hantavirus galibi tana yaduwa ne ta hanyar cudanya da beraye masu ɗauke da cutar, yayin da alamomin ta kan bayyana tsakanin mako guda zuwa takwas bayan kamuwa.
A lokuta masu tsanani, cutar na iya janyo matsalar numfashi ko lalacewar koda. Sai dai kariya daga cutar ta ta’allaka ne kan tsafta da yaki da beraye, domin har yanzu babu rigakafi ko wani takamaiman magani da aka amince da shi.
