2027: Dr. Kabir Ya Sayi Fom Din Takarar ADC na Mazaɓar Kaltungo/Shongom

Kabir Abubakar Khiga ya sayi fom din tsayawa takara a karkashin jam’iyyar African Democratic Congress (ADC) domin neman kujerar wakilcin mazabar tarayya ta Kaltungo/Shongom a Majalisar Wakilai ta Kasa.

Khiga ya sayi fom din ne a ranar Juma’a, 8 ga watan Mayun shekarar 2026, a wani mataki da ke nuna aniyarsa ta shiga fafatawar siyasa domin wakiltar al’ummar mazabar.

Da yake magana bayan sayen fom din, ya yi alkawarin tabbatar da adalci da daidaito ga daukacin al’ummar mazabar Kaltungo/Shongom ba tare da nuna bambanci ba.

Ya ce idan aka ba shi dama ya wakilci al’umma, zai mayar da hankali wajen kare muradun jama’a, bunkasa ci gaba, da kuma tabbatar da cewa an gudanar da shugabanci nagari mai anfani ga kowa da kowa.

Ya kuma jaddada bukatar hadin kai tsakanin al’umma domin samun ci gaba mai dorewa, “yana mai cewa siyasa ya kamata ta kasance hanyar kawo cigaba da zaman lafiya ga jama’a”.

Masu goyon bayansa sun bayyana farin cikinsu kan matakin da ya dauka, suna mai bayyana shi a matsayin mutum mai hangen nesa da kishin ci gaban mazabar Kaltungo/Shongom.

Ana sa ran cewa takarar tasa za ta ƙara zafafa fafatawar siyasa a yankin yayin da jam’iyyun siyasa ke ci gaba da shirye-shiryen tunkarar zabukan shekarar 2027.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *