2027: Ban Mara wa Gubio Baya Kawai ba, Shine Zaɓi na – Zulum

Babagana Umara Zulum, Gwamnan Jihar Borno

Gwamnan Jihar Borno, Babagana Umara Zulum, ya bayyana cewa ya “naɗa” tsohon Kwamishinan Ayyuka da Gidaje na jihar, Injiniya Mustapha Gubio, a matsayin ɗan takarar gwamna na shekarar 2027.

A cikin wata sanarwa da mai ba gwamna shawara kan harkokin yaɗa labarai, Dauda Illiya, ya fitar a ranar Laraba, ya ce gwamnan ya yi amfani da kalmar “naɗa” ne kawai yayin wata ganawar siyasa da aka gudanar a Abuja.

Sanarwar mai taken “Zulum anoints, not endorses Gubio as his successor” ta bayyana cewa matakin da gwamnan ya ɗauka wani ɓangare ne na al’adar siyasa da aka saba.

Illiya ya ce, “Karɓar ‘yan takara al’ada ce ta shugabanni nagari domin yi musu fatan alheri da addu’ar nasara a tsarin dimokuraɗiyya.”

Ya ƙara da cewa gwamnan, a matsayinsa na jagoran jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a jihar, ya kuma karɓi wasu ‘yan takara daban-daban, ciki har da masu neman kujerar Sanatan Borno ta Arewa da kuma ‘yan Majalisar Wakilai, waɗanda suka gabatar da fom ɗin su na takara.

A cewarsa, “Gwamna Zulum bai tsaya kan karɓar Injiniya Gubio kaɗai ba—wanda shi ne na farko da ya sayi fom ɗin nuna sha’awa da na tsayawa takara—har ma ya karɓi Sanata Mohammed Tahir Monguno da ke neman sake tsayawa takarar Sanatan Borno ta Arewa, da kuma ɗan Majalisar Wakilai mai wakiltar Monguno/Nganzai/Marte, Hon. Bukar Talba, da sauran su.”

Illiya ya jaddada cewa gwamnan “mai cikakken kishin dimokuraɗiyya ne wanda ke goyon bayan haɗa kowa da kowa,” yana mai cewa tun a ranar 25 ga Afrilu, a wani taro da aka yi a gidan gwamnati, ya sanar da masu ruwa da tsaki cewa za a sake yin wani zama domin gabatar da ‘yan takarar jam’iyyar a hukumance.

Sai dai wani malamin kimiyyar siyasa a Federal University Gashu, Lawan Cheri, ya bayyana cewa kalmar “goyon baya” (endorsement) da “naɗawa” (anointment) ba iri ɗaya ba ne, duk da cewa suna iya kama da juna.

A cewarsa, “Goyon baya bayyana ne a fili na goyon bayan wani bisa la’akari da tsari, daidaiton manufofi ko biyayya ga jam’iyya. Amma naɗawa na ɗauke da ma’ana ta zaɓen mutum ta musamman daga shugaba ko wani iko mafi girma, tare da tasirin ra’ayi na zuciya.”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *