Rikicin Shugabanc ADC: Kotun ta Sanya Ranar Alhamis Don Yanke Hukunci

Kotun Koli ta sanya ranar Alhamis, 30 ga Afrilu, domin yanke hukunci a rikicin shugabanci da ke addabar jam’iyyar adawa ta African Democratic Congress (ADC).

Tun da farko kotun koli ta ajiye hukunci kan shari’ar, lamarin da ya sa jam’iyyar ta rubuta koke ga Babban Alƙalin Ƙasa (CJN), tana mai cewa lokaci ba ya gefe nasu.

Sai dai a ranar Laraba, kotun ta sanar da cewa za a yanke hukuncin da misalin ƙarfe 2 na rana a ranar Alhamis.

Kwamitin alƙalai biyar na kotun, ƙarƙashin jagorancin Mai shari’a Mohammed Garba, ne ya sanya ranar yanke hukuncin bayan ɓangarorin shari’ar sun kammala gabatar da hujjojin su na ƙarshe a rubuce.

David Mark, wanda ke jagorantar wani ɓangare na jam’iyyar, na ƙalubalantar hukuncin Kotun Ɗaukaka Ƙara na ranar 12 ga Maris, wanda ya umarci ɓangarorin su ci gaba da kasancewa yadda suke (status quo) a cikin rikicin.

A cikin ƙorafinsa, tsohon shugaban majalisar dattawan ya ce kotun ɗaukaka ƙara ta wuce ikon ta, yana mai jaddada cewa rikicin na cikin harkokin cikin gida na jam’iyya ne, wanda kotuna ba su da ikon yanke hukunci a kai.

An shigar da ƙarar ne daga wasu mambobin jam’iyyar da ba su gamsu ba, ƙarƙashin jagorancin Nafiu Bala Gombe, wanda ke ƙalubalantar sahihancin shugabancin ɓangaren da Mark ke jagoranta.

Sauran waɗanda ke cikin shari’ar sun haɗa da jam’iyyar ADC, sakatarenta na ƙasa Rauf Aregbesola, da Independent National Electoral Commission (INEC), da kuma tsohon shugaban jam’iyyar na ƙasa Ralph Nwosu.

Mark na kuma neman umarnin kotu da zai hana INEC amincewa da kowace shugabanci banda ɓangaren da yake jagoranta, har sai an yanke hukunci kan ɗaukaka ƙarar.

Sai dai ɓangarorin da ake ƙara sun roƙi kotun koli da ta yi watsi da ƙarar, suna masu cewa kotun ƙasa ta yi aiki bisa ƙa’ida.

ƙarin bayani nan gaba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *