Aron Katin Waya: Kotu Ta Dakatar da Yunkurin Kamfanonin Sadarwa na Katse Sabis

Miliyoyin masu amfani da layukan sadarwa a Najeriya na iya sake samun damar amfani da sabis ɗin aron katin waya da data, bayan umarnin kotunan tarayya daban-daban a Abuja da Legas da suka dakatar da aiwatar da wasu sabbin dokokin lamuni na dijital.

A Abuja, kotu ta yanke hukunci a ranar 24 ga Afrilu, 2026 cewa MTN Nigeria da Airtel Networks ba za su dakatar ko takaita ayyukan da suke yi wa kamfanin Nairtime Nigeria Limited ba, har sai an kammala sauraron ƙarar da ke ƙalubalantar umarnin da ke da alaƙa da dokokin Digital, Electronic, Online or Non-Traditional Consumer Lending Regulations (DEON) 2025.

Masu ƙarar sun bayyana cewa shirin dakatar da ayyukan USSD, saƙonnin SMS, lambobin gajere (short codes) da kuma tsarin cajin kuɗi zai saba wa haƙƙoƙinsu na kwangila.

Kotun ta amince da hujjojin, inda ta bayar da umarnin wucin gadi (injunction) domin tabbatar da ci gaba da ba da sabis ɗin yayin da lasisin Nairtime ke nan daram.

Alƙalin ya jaddada cewa kamfanonin sadarwa ba za su iya kauce wa sharuddan sanarwa ko hanyoyin warware rikici da aka amince da su ba kawai don bin sabbin dokoki.

Haka kuma, kotun tarayya da ke Legas ta yanke hukunci a ranar 15 ga Afrilu, 2026, inda ta hana Federal Competition and Consumer Protection Commission (FCCPC) aiwatar da wasu muhimman sassan dokokin DEON a kan ƙungiyar masu samar da ayyukan sadarwa ta Wireless Application Service Providers Association of Nigeria.

Mai shari’a Ambrose Lewis-Allagoa ya hana hukumar ɗaukar matakin hukunci ko kawo cikas ga masu ba da sabis har sai an saurari buƙatar cikakken umarni.

Wannan hukunci na zuwa ne bayan MTN Nigeria da Airtel Networks sun dakatar da sabis ɗin aron kati a tsakiyar watan Afrilu, suna mai cewa suna bin sabbin dokokin da aka ƙirƙira.

Dakatarwar ta shafi miliyoyin masu amfani da layin biya-gaba (prepaid) da ke dogaro da aron kati a matsayin ƙaramar hanya ta samun bashi na ɗan lokaci.

Masu ruwa da tsaki a masana’antar sun ce FCCPC ta wuce ikon da aka ba ta, suna mai cewa irin waɗannan ayyuka na sadarwa suna ƙarƙashin kulawar Nigerian Communications Commission (NCC).

Masana sun kiyasta cewa kasuwancin aron katin waya na da darajar tsakanin naira biliyan ₦500 zuwa tiriliyan ₦1.2 a duk shekara, kuma yana taka muhimmiyar rawa a matsayin ƙaramin bashi ga ƙananan ‘yan kasuwa da masu ƙaramin ƙarfi na tattalin arziki.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *