Gwamnan jihar Oyo, Seyi Makinde, ya yi nuni da tarihin tashin hankalin siyasa na “Operation Wetie” domin yin gargaɗi kan yunƙurin kafa mulkin jam’iyya ɗaya a Najeriya.
“Operation Wetie” wani yanayi ne na tashin hankali mai tsanani da ya auku a yankin Yammacin Najeriya a tsakiyar shekarun 1960, musamman a birnin Ibadan. Kalmar ta samo asali ne daga harshen Yarbanci, ma’ana “a jika shi,” inda ake zuba fetur a kan abokan hamayya na siyasa ko kadarorinsu kafin a banka musu wuta.
Lamarin ya ɓarke ne bayan zaɓen yankin Yamma na 1965, wanda aka zarge shi da maguɗi domin fifita ɓangaren da ke mulki tare da danne ‘yan adawa.
Da yake jawabi a taron ƙasa na shugabannin jam’iyyun adawa da aka gudanar a Ibadan, Makinde ya nuna damuwa kan ƙoƙarin da ake yi na ƙarfafa iko a majalisu a hannun jam’iyya ɗaya, yayin da jam’iyyun adawa ke fama da rikice-rikicen cikin gida da shari’o’i.
“Ga waɗanda ke tafiya kamar babu gobe, su tuna cewa ‘operation wetie’ ta fara ne daga nan. Wannan shi ne tsohon ‘Wild Wild West’ ɗin nan,” in ji Makinde.
Ya ƙara da cewa a shekarar 1950, Ibadan ta karɓi muhimman tattaunawa da suka taimaka wajen tsara makomar kundin tsarin mulkin Najeriya, yana mai cewa irin wannan taro na yanzu na da nauyin irin wancan tarihi.
Makinde ya ce akwai yunƙuri a bayyane na tattara ikon majalisu a ƙarƙashin jam’iyya ɗaya, yayin da jam’iyyun adawa ke fuskantar matsaloli da ke jefa shakku kan ingancinsu.
Ya gargadi cewa bai kamata a ɗauki irin waɗannan abubuwa da wasa ba, yana mai cewa lokaci ne da ya kamata shugabannin adawa su ƙara shiga harkokin siyasa da ƙarfi.
“Ba abu ne da ya kamata mu ɗauka da wasa ba. Ba na tunanin akwai masu zagon ƙasa a nan, amma dimokuraɗiyya ba ta rushewa a rana ɗaya; ana raunana ta ne sannu a hankali har sai jama’a sun fara jin ba ta aiki a gare su,” in ji shi.
Ya ƙara da cewa idan jam’iyyun adawa suka zama marasa ƙarfi, to dimokuraɗiyya kanta na rasa ma’anarta, domin dimokuraɗiyya na nufin samuwar zaɓuɓɓuka ga jama’a.
Makinde ya jaddada cewa taron ba wai don adawa da wani mutum bane ko kuma burin mutum ɗaya na zama shugaban ƙasa.
“Wannan taro ba wata haɗakar kai ba ce domin adawa da wani mutum, kuma ba don burin mutum ɗaya ba ne. Manufarsa ita ce samar da dimokuraɗiyya mai inganci ga ‘yan Najeriya,” in ji shi.
Ya kuma ce ko da jam’iyya ta yi ƙarfi ko gwamnati ta samu karɓuwa, samuwar ingantacciyar adawa ba barazana ba ce ga dimokuraɗiyya, illa ma ginshiƙi ne na dorewarta.
