Ƙasashen mambobin ECOWAS an buƙace su da su tsawaita hutun haihuwa zuwa watanni shida domin inganta rayuwar yara da lafiyar iyaye mata.
An bayyana wannan kira ne ta bakin Dakta Virgil Lokossou, Daraktan Ayyukan Kiwon Lafiya na Hukumar Lafiya ta Yammacin Afirka (WAHO), yayin wani taron yanar gizo na yankin kan lafiyar uwa, jarirai da yara, wanda aka gudanar a matsayin wani ɓangare na zama na 27 na ministocin lafiya na ECOWAS a Freetown, Saliyo.
Lokossou ya jaddada cewa shayar da jariri nono kaɗai na tsawon watanni shida na daga cikin hanyoyi mafi inganci kuma mafi arha wajen rage cututtuka da mace-macen yara, tare da taimakawa lafiyar uwa bayan haihuwa.
Ya ce, “Daidaita dokokin ƙwadago na ƙasa da shawarwarin duniya na shayar da jariri nono kaɗai na tsawon watanni shida na buƙatar ɗaukar matakai masu ƙarfi, musamman wajen tsawaita hutun haihuwa mai albashi da kuma samar da yanayi mai dacewa ga mata masu shayarwa.”
Ya ƙara da cewa dole ne gwamnatoci su tabbatar da cewa manufofin wuraren aiki da tsarin kariyar jama’a suna la’akari da bukatun mata, tare da kira ga masu daukar ma’aikata su rungumi tsare-tsare masu taimaka wa iyali kamar sassauta lokacin aiki da samar da wurare masu aminci don shayarwa.
Tattaunawar ta kuma jaddada buƙatar tara kuɗaɗen cikin gida domin fannin lafiya, inda mahalarta suka yi kira ga samar da sabbin hanyoyin samun kuɗi kamar haraji na musamman don lafiya da kuma asusun lafiya na al’umma.
An kuma buƙaci ‘yan majalisa su mayar da shawarwarin yankin zuwa dokoki masu ƙarfi a ƙasashensu, musamman waɗanda ke kare mata da yara.
Rahotanni daga wasu ƙasashe sun nuna cewa ana samun ƙara ƙwazo wajen ɗaukar waɗannan matakai.
Masana sun bayyana cewa inganta shayar da jarirai nono zai iya rage mace-macen yara ‘yan ƙasa da shekaru biyar a Yammacin Afirka, inda har yanzu ake samun yawan mace-mace daga cututtukan da za a iya kauce wa.
A Najeriya, hutun haihuwa a yawancin fannoni bai kai watanni shida ba, lamarin da masana ke cewa na iya hana samun cikakkiyar shayarwa da kuma kyakkyawan lafiyar yara.
