Farfesa Wellington Oyibo, kwararren masanin cututtukan ƙwayoyin halitta a Jami’ar Legas, ya yi gargadin cewa zazzabin cizon sauro da ba a yi masa magani ba na daga cikin manyan dalilan zubar ciki da matsalolin lafiya ga mata masu juna biyu a Najeriya.
Da yake magana gabanin Ranar Yaki da Zazzabin Cizon Sauro ta Duniya (25 ga Afrilu, 2026), Oyibo ya buƙaci mata masu juna biyu su riƙa amfani da gidan sauro mai maganin kashe ƙwari, su fara zuwa duba ciki da wuri, tare da yin gwajin cutar domin kare kansu da jariransu.
Ya bayyana cewa ƙwayoyin cutar zazzabin cizon sauro, musamman Plasmodium falciparum da P. vivax, na iya kai hari ga mahaifa (placenta), wanda hakan ke janyo zubar ciki, mutuwar jariri a ciki, haihuwa kafin lokaci, da kuma ƙarancin nauyin jariri.
A cewarsa, “ƙwayar cutar na zuwa mahaifa, tana lalata ta, tana kuma haddasa ƙarancin jini ga uwa. Wannan na hana jariri samun isassun sinadirai, yana kawo tangarɗa ga girma, har ma ya kai ga haihuwa kafin lokaci.”
Oyibo ya bayyana cutar zazzabin cizon sauro a matsayin mai “mugunta,” yana mai cewa tana iya yaɗuwa zuwa ga jariri har ma ta kai ga kwakwalwa, inda take haddasa mummunar cutar da ake kira cerebral malaria. Ya jaddada muhimmancin yin rajistar duba ciki da wuri domin samun kariya.
Ya kuma nuna cewa gwamnati na aiwatar da wasu matakai kamar raba gidajen sauro ga mata masu juna biyu, amma ya ce wayar da kai da kuma ɗaukar matakin kariya da kai na da matuƙar muhimmanci.
Oyibo ya shawarci mata su riƙa yin gwaji kafin shan maganin zazzabin cizon sauro, yana mai cewa kariya na farawa ne daga gida. “Mu fara kariya tun daga farko, mu riƙa amfani da gidan sauro; kariya tana farawa ne daga gida,” in ji shi.
A ƙarshe, ya yi kira da a ƙara ƙoƙari wajen yaƙi da zazzabin cizon sauro, yana mai cewa kariya daga cutar na da muhimmanci ba kawai ga lafiyar uwa ba, har ma don rage yawan mace-macen mata masu juna biyu a Najeriya.
