ACPN Ta Goyi Bayan Haramcin Magunguna ta Nemi Samar da Kashi 70% a Cikin Gida

Ƙungiyar Masu Magungunan Al’umma ta Najeriya (ACPN) ta yabawa Gwamnatin Tarayya kan sabunta jerin kayayyakin da aka haramta shigowa da su, tana mai cewa hakan zai ƙarfafa samar da magunguna a cikin gida da kuma inganta tsaron lafiyar al’umma.

A wata sanarwa da shugabannin ƙungiyar suka fitar, sun ce takaita shigo da magungunan da za a iya samarwa a cikin gida zai rage asarar kuɗaɗen waje tare da ƙarfafa tsarin kiwon lafiya.

Haramcin ya shafi magunguna kamar paracetamol, metronidazole, chloroquine, aspirin, folic acid da wasu man shafawa. ACPN ta ce matakin zai ƙara ɗora nauyi kan masana’antun cikin gida domin su cika buƙatun kiwon lafiya.

Ƙungiyar ta kuma buƙaci Hukumar Kwastam ta tabbatar da aiwatar da dokar cikin gaskiya, tare da guje wa kama kaya ba bisa ƙa’ida ba. Ta ƙara da cewa rage haraji kan magunguna zai taimaka wajen sauƙaƙa farashi da samun su ga jama’a.

A halin yanzu, Najeriya na shigo da kusan kashi 65% na magunguna daga waje. ACPN ta yi gargaɗin cewa dogaro da shigo da magunguna na iya jefa ƙasar cikin haɗari kamar yaduwar magungunan jabu da tangardar samar da su.

Ƙungiyar ta nuna fata cewa da inganta masana’antu fiye da 120 da ke ƙasar, Najeriya za ta iya cimma burin samar da kashi 70% na magunguna a cikin gida nan da 2030. Ta kuma yi kira da a ƙarfafa dokoki da hukunci kan masu safarar magungunan jabu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *