Trends

Air Peace za ta Fara Zuwa London Daga Sabon Filin Jirgin Ogun

Kamfanin jiragen sama na Air Peace ya sanar da shirinsa na fara zirga-zirgar jirage zuwa birnin London daga sabon filin jirgin sama na Gateway International Airport a lokacin bazara mai zuwa.

Babban jami’in kamfanin (CEO), Allen Onyema, ne ya bayyana wannan shiri yayin kaddamar da filin jirgin, inda ya bayyana shi a matsayin daya daga cikin filayen jiragen sama mafi inganci a yankin Afirka ta Kudu da Sahara.

Onyema ya yabawa gwamnatin jihar Ogun bisa kammala wannan aiki, yana mai cewa filin jirgin ya yi daidai da na kasashen da suka ci gaba.
Ya ce, “Ba gini kawai ba ne; ya kunshi duk abin da ake bukata domin cikakken filin jirgin sama.”

Ya kuma tabbatar da cewa kamfanin Air Peace ya samu amincewar Ma’aikatar Sufurin Jiragen Sama ta Tarayya domin fara zirga-zirgar jiragen kasa da kasa daga filin jirgin.

“A karkashin gayyatar gwamnan jihar, za mu fara zirga-zirgar jirage daga nan zuwa London Gatwick Airport da Heathrow Airport a wannan bazara,” in ji Onyema.

Ya kara da cewa kamfanin zai tabbatar da an yi amfani da filin jirgin yadda ya kamata, yana mai jaddada cewa wannan aiki zai amfani ba jihar Ogun kadai ba har ma da daukacin Najeriya.
Ministan Sufurin Jiragen Sama, Festus Keyamo, shi ma ya bai wa kamfanin izinin fara aiki a sabon filin jirgin.

Wannan ci gaba na nuna wani muhimmin mataki ga bangaren sufurin jiragen sama na jihar Ogun, inda ake sa ran filin jirgin na Gateway International Airport zai zama cibiyar zirga-zirgar jiragen kasa da kasa, tare da kara hada Najeriya da kasashen Turai.