Trends

Taraba Ta Yi Asarar Rayuka 50 Sakamakon Barkewar Zazzabin Lassa

147509621

Asibitin Kasa (FMC) da ke Jalingo ya tabbatar da mutuwar mutane 50 sakamakon cutar Lassa fever, lamarin da ya zama mafi muni da cibiyar ta taba fuskanta a shekarun baya-bayan nan.

“Wannan shi ne mafi girman adadin wadanda ake zargi da kamuwa da cutar da kuma mace-macen da muka taba samu a wannan cibiyar,” in ji Dakta Suleiman Abubakar Kirim, Shugaban Sashen Kula da Marasa Lafiya.

A cewarsa, an kwantar da mutane 226 da ake zargin sun kamu da cutar, inda 95 daga cikinsu aka tabbatar da kamuwar su ta gwaje-gwaje. Daga cikin wadanda aka tabbatar, mutane 50 sun rasu, yayin da wasu 20 suka warke aka sallame su. Ya kara da cewa har yanzu ana ci gaba da samun sabbin masu kamuwa da cutar.

Likitan ya nuna fatan cewa yaduwar cutar za ta ragu da fara damina, yana mai bayanin cewa cutar na yaduwa sosai a lokacin rani.

Ya ce, “Muna sa ran yawan kamuwa da cutar zai ragu yayin da damina ta fara.”
Hukumar asibitin ta kuma bayyana cewa an fara amfani da sabbin kayan aiki na musamman (service packs) domin inganta tsaro da ingancin aiki a fannin kiwon lafiya.

“Wadannan kayan suna tabbatar da daidaito, inganci da kuma hana yaduwar cututtuka ta hanyar samar da kayayyakin da aka tsabtace,” in ji hukumar.

Jami’an sun yi gargadin cewa amfani da kayan da ake ta maimaita amfani da su na kara haɗarin yaduwar cuta ga ma’aikatan lafiya da marasa lafiya.
“Saboda haka, service packs na zama muhimmin matakin kariya ga marasa lafiya da ma’aikatan asibiti,” in ji asibitin.

Hukumar ta kara da cewa irin wannan tsari na daga cikin hanyoyin da ake amfani da su a manyan asibitoci a Najeriya da kuma kasashen waje kamar Ghana, Amurka, Indiya da Afirka ta Kudu.

Sun ce wannan hanya na da matukar muhimmanci musamman a lokutan barkewar cututtuka kamar zazzabin Lassa.

A karshe, FMC Jalingo ta bukaci jama’a da su rika amfani da hanyoyin hukuma kamar sashen SERVICOM wajen neman bayani ko gabatar da koke-koke.

“Duk wanda ke bukatar karin bayani kan harkokin kiwon lafiya ya kamata ya bi hanyoyin hukuma kafin yanke hukunci,” in ji asibitin, yana gargadin cewa kalaman da ba su da tushe na iya rage amincewar jama’a da tsarin lafiya.