Trends

Bankin Duniya Ya Amince da Bashin Dala Miliyan 500 Domin Noma a Najeriya

capital, business, finance, economy, banking and money concept 3D rendering animation.

Bankin Duniya ya amince da bayar da bashin dala miliyan 500 ta hannun Hukumar International Development Association (IDA) domin bunƙasa harkar noma a Najeriya karkashin sabon shirin Nigeria Sustainable Agricultural Value Chains for Growth Project (AGROW).

Shirin na da nufin ƙara yawan amfanin gona, ƙarfafa sarkar darajar noma, da kuma inganta wadatar abinci a ƙasar.

A wata sanarwa da bankin ya fitar, ya ce noma na ci gaba da kasancewa babbar hanyar samar da ayyukan yi a Najeriya, amma ƙarancin yawan amfanin gona, rashin samun ingantattun kayan aiki, sauyin yanayi, da raunin haɗin kasuwanni sun takaita damar da fannin ke da ita. An amince da bashin ne a ranar 30 ga Maris, 2026.

Shirin AGROW zai tallafa wa kamfanonin kasuwancin noma da ke sayen amfanin gona daga ƙananan manoma ta hanyar tallafin kuɗi bisa sakamako (matching grants).

Amfanin gona da aka bai wa fifiko sun haɗa da shinkafa, masara, rogo, da waken soya. Haka kuma, shirin zai mai da hankali kan tattara amfanin gona, sarrafa su bayan girbi, sarrafa su zuwa kayayyaki, da kuma inganta hanyoyin kai su kasuwa.

Haka zalika, shirin zai ƙarfafa bincike da ayyukan wayar da kai ga manoma, ƙara samun iri masu jure sauyin yanayi, da kuma kafa rajistar ƙasa ta manoma da gonaki ta hanyar fasahar zamani.
Manoma za su amfana da shawarwari ta hanyar fasaha, ciki har da bayanan yanayi da na sauyin yanayi da aka daidaita da wurarensu.

Bankin ya kuma bayyana cewa shirin zai inganta tsarin kula da ingancin iri da taki, ƙara samar da iri na farko (early-generation seeds), da kuma ƙarfafa kamfanoni masu zaman kansu wajen samar da ingantattun kayan noma.

An jaddada muhimmancin haɗa mata da matasa cikin shirin, tare da samar da ingantaccen tsarin sa ido da kuma bai wa al’umma damar sa ido kan yadda ake gudanar da shi.

Daraktan Bankin Duniya a Najeriya, Mathew Verghis, ya bayyana AGROW a matsayin wani babban sauyi ga harkar noma.

Ya ce, “AGROW wani babban mataki ne da zai sauya fannin noma a Najeriya—yana ƙarfafa ƙananan manoma, buɗe damar ci gaban da kamfanoni masu zaman kansu ke jagoranta, tare da ƙarfafa wadatar abinci ta hanya mai ɗorewa.”

Ana sa ran shirin zai amfanar da kusan manoma miliyan ɗaya, tare da jawo jarin kamfanoni masu zaman kansu da ya kai dala miliyan 220.