Tsohon mai ba Gwamnan Jihar Kano shawara kan harkokin yada labarai da sadarwa a zamanin Abdullahi Ganduje, wato Dawisu Yakasai, ya sanar da ficewarsa daga jam’iyyar All Progressives Congress (APC) tare da komawa African Democratic Congress (ADC).
Yakasai ya bayyana hakan ne a ranar Litinin ta shafinsa na X mai suna @dawisu, inda ya ce ya kammala shirye-shiryen komawa ADC a matsayin wani sabon alkibla a siyasarsa.
A cewarsa, wannan mataki ya biyo bayan dogon shawarwari da ya yi da iyali, abokai da kuma abokan siyasa da suka dade suna aiki tare.
Ya rubuta cewa: “Bayan tuntuba mai zurfi da iyali, abokai da abokan siyasa da muka dade muna aiki tare, mun yanke shawarar komawa ADC a matsayin sabon alkibla.”
“Na mika takardar ficewa daga APC kuma na kammala rajista da sabuwar jam’iyyarmu ta ADC,” in ji shi.
Yakasai ya kuma tabbatar da cewa ya riga ya yi rajista a hukumance da ADC, tare da kira ga magoya bayansa da ke da sha’awar shiga jam’iyyar da su cika rajistarsu ta yanar gizo.
Haka kuma ya nuna fatan alheri ga jam’iyyar ADC, yana rokon Allah ya ba ta nasara da shiriya a dukkan matakan gwamnati.
Wannan sauyin na siyasa na zuwa ne a daidai lokacin da harkokin siyasa ke kara daukar sabon salo a Jihar Kano, gabanin zabukan da ke tafe.
