Dangote Ya Kara Farashin Man Fetur zuwa ₦1,245 kan Lita

Dangote Petroleum Refinery ta sanar da karin farashin man fetur (PMS), inda ta daga farashin daga ₦1,175 zuwa ₦1,245 kan kowace lita, wanda zai fara aiki daga tsakar dare na ranar 21 ga Maris, 2026.

Matatar ta bayyana cewa karin farashin ya biyo bayan yanayin kasuwar duniya, ciki har da tashin farashin danyen mai da ya haura dala $100 kan kowace ganga, da kuma karin kudin jigilar kaya sakamakon rikicin Gabas ta Tsakiya.

An ce ‘yan kasuwa da ke da tabbacin banki (bank guarantee) za su iya ci gaba da karbar kaya a tsohon farashi, amma za a cire bambancin kudin daga asusun su, tare da bukatar su gabatar da shaidar biyan kudin kafin ranar 23 ga Maris.

Duk da karin, Dangote ta jaddada cewa Najeriya na daya daga cikin kasashen da ke da mafi karancin farashin fetur a duniya. Ta ce, “A halin yanzu farashin fetur a Najeriya na kusan $0.88 (₦1,191.39) kan lita, wanda ya yi kasa da matsakaicin farashin duniya na $1.32 (₦1,787.08).”

Kwatantawa ta nuna cewa farashin ya fi tsada a kasashe kamar Amurka ($1.075), Indiya ($1.095), da Afirka ta Kudu ($1.189), yayin da a Turai farashin ya fi tsanani, inda Birtaniya ke da $1.874, Jamus kuma $2.343 kan kowace lita. A yankin Yammacin Afirka kuwa, farashin fetur a Najeriya ya fi rahusa idan aka kwatanta da Togo, Benin, Ghana da Kamaru.

Masana tattalin arziki sun yaba wa matatar bisa rage tasirin tashin farashi a cikin gida, duk da rikice-rikicen samar da mai a kasuwar duniya. Sai dai wannan shi ne karo na hudu da aka kara farashi a watan Maris, inda PMS ya tashi daga ₦774 a farkon watan zuwa ₦1,245 a yanzu.

Karuwar ta biyo bayan tashin farashin danyen mai na Brent zuwa $112 kan ganga, mafi girma tun tsakiyar shekarar 2022, yayin da Najeriya ke fama da gazawar cika adadin da OPEC ta kayyade mata, inda ta samar da ganga miliyan 1.31 a rana a watan Fabrairu.

Ana sa ran karin kudin sufuri da farashin kayayyaki zai biyo baya, yayin da wasu kasashen Afirka, ciki har da Afirka ta Kudu, Ghana da Kenya, suka tuntubi matatar Dangote domin samun man fetur sakamakon karancin mai a duniya.