Najeriya na shirin jawo jarin kusan dala miliyan 200 bayan wata sabuwar yarjejeniya tsakanin kamfanin Nigus International Investment Limited da kamfanin Elmirate Investment LLC (Elmirate Capital) na Hadaddiyar Daular Larabawa.
Kamfanonin biyu sun rattaba hannu kan yarjejeniyar fahimtar juna (MoU) domin kafa wata cibiyar fasaha ta zamani da masana’antu masu inganci a Najeriya.
Shirin zai mayar da hankali kan fasahar tsaro, inganta kariyar yanar gizo (cybersecurity), da kuma harkokin tauraron dan adam, domin karfafa samar da kayayyakin tsaro a cikin gida da kuma bunkasa tsarin tsaron dijital na kasar.
Shugaban zartarwa na kamfanin Nigus International, Yarima Malik Ado-Ibrahim, ya bayyana cewa wannan shiri na nuna yadda Afirka ke kara fahimtar alakar da ke tsakanin fasaha, karfin tattalin arziki, da tsaron kasa.
“Afrika na shiga wani muhimmin mataki na ci gaba, inda fasaha za ta kara zama ginshiki wajen karfin tattalin arziki da kuma tsaron kasa,” in ji Ado-Ibrahim.
Ana sa ran hadin gwiwar zai kara karfin Najeriya a fannin fasahar sararin samaniya, ya inganta kariya daga barazanar hare-haren yanar gizo, tare da bunkasa masana’antu a cikin gida.
Jami’ai sun kuma bayyana cewa wannan yarjejeniya za ta taimaka wajen kara matsayin Najeriya a kasuwar duniya ta fannin tsaro da fasaha, tare da samar da damammaki ga hazikan matasa da kirkire-kirkire na cikin gida.
Yarjejeniyar MoU na nuna kokarin Najeriya na kara jawo jari daga kasashen waje musamman a fannoni masu muhimmanci da za su bunkasa tattalin arziki da tsaron kasa na dogon lokaci.
