Trends

Kuɗin Mita: NERC Ta Umarci Kamfanonin Wutar Lantarki Su Mayar da N20B

Hukumar Kula da Harkokin Wutar Lantarki ta Najeriya (NERC) ta umurci dukkan kamfanonin rarraba wutar lantarki (DisCos) da su mayar wa kwastomomi Naira biliyan 20.33 na kuɗin mitoci da ake binsu a ƙarƙashin tsarin Meter Asset Provider (MAP).

Hukumar ta bayyana cewa dole ne a kammala mayar da kuɗaɗen cikin watanni 12, daga ranar 1 ga Maris, 2026, bayan ta gudanar da nazari kan yadda aka bi ƙa’idoji tare da gano cewa kamfanonin sun gaza mayar wa kwastomomi kuɗin mitocin da suka saya a tsarin.

A ƙarƙashin tsarin MAP, kwastomomi ne ke biyan kuɗin mita tun farko, sannan a mayar musu ta hanyar basussukan makamashi (energy credits) a hankali. NERC ta ce an samu jinkiri mai yawa a biya, lamarin da ya sa aka fitar da sabon umarni domin tilasta bin doka da kuma dawo da amincewa a fannin wutar lantarki.

Umurnin mai lamba NERC/2026/025, wanda Shugaban Hukumar, Musiliu Oseni, da Kwamishina Dafe Akpeneye suka sanya wa hannu, ya wajabta cewa duk mayar da kuɗin dole ne ya kasance ta hanyar tsarin atomatik a asusun kwastomomi.

“Dole ne DisCos su tabbatar da cewa jimillar kuɗin mita na MAP an sanya shi a matsayin bashi (credit) a asusun kwastoma nan da nan bayan an kunna mitar,” in ji umarnin.

Ga kwastomomin da ke amfani da mita na prepaid, za a riƙa samar musu da tokens na wata-wata daidai da kuɗin da ake mayar musu ta atomatik. Ga masu amfani da postpaid kuwa, za su ga layin bashi na musamman a cikin takardar kuɗinsu. Haka kuma, an hana kamfanonin rage kuɗin mitar da ake biya da wasu tsofaffin basussuka.

Domin warware tsofaffin bashin da ake bi, an umurci DisCos da su hanzarta biyan kuɗin, inda kwastomomin prepaid za su riƙa karɓar tokens biyu a kowane wata, yayin da masu postpaid za su ga layukan bashi biyu a takardunsu har sai an kammala biya.

NERC ta kuma wajabta a riƙa gabatar da rahoton wata-wata tare da buɗe wata hanyar karɓar ƙorafi ta musamman.

“Dukkan DisCos dole ne su riƙa gabatar da rahoton wata-wata… sannan su samar da adireshin imel na musamman domin karɓar ƙorafin kwastomomin da ba su samu mayar da kuɗin mitar MAP ba,” in ji umarnin.

Hukumar ta ce wannan mataki na da nufin hana maimaita jinkiri, ƙarfafa ɗaukar alhaki, da kuma inganta amincin fannin wutar lantarki a Najeriya.