Kuɗaɗen Harajin Ƙara Daraja (VAT) na Nijeriya sun ƙaru zuwa naira tiriliyan 2.28 a kashi na uku (Q3) na shekarar 2025, wanda ya nuna ƙarin kashi 10.66 cikin 100 idan aka kwatanta da naira tiriliyan 2.06 da aka samu a kashi na biyu na shekarar, a cewar Hukumar Ƙididdiga ta Ƙasa (NBS).
An bayyana hakan ne a cikin rahoton “Rarraba VAT Bisa Sassa – Q3 2025” da hukumar ta fitar ranar Talata. Idan aka kwatanta da makamancin lokacin shekarar 2024 (Q3 2024), kuɗaɗen VAT sun ƙaru da kashi 28.10 cikin 100.
Rahoton ya ce, “Kuɗaɗen Harajin Ƙara Daraja (VAT) a kashi na uku na 2025 sun kai naira tiriliyan 2.28, wanda ya nuna ƙarin kashi 10.66 bisa dari idan aka duba daga kashi zuwa kashi.”
Biyan VAT na cikin gida ne ya fi yawa, inda ya kai naira tiriliyan 1.12. VAT daga waje ya bayar da gudunmawar naira biliyan 680.23, yayin da VAT kan kayayyakin da aka shigo da su ya kai naira biliyan 479.79.
A bangaren bunƙasar sassa, ayyukan gudanarwa da tallafi (administrative and support services) sun fi kowa samun haɓaka da kashi 89.28 cikin 100. Sai kuma fannin fasaha, nishaɗi da wasanni da kashi 82.49, sannan ayyukan lafiya da jin ƙai da kashi 32.40.
A gefe guda kuma, fannin gidaje (real estate) shi ne ya fi samun koma baya da kashi –51.33 cikin 100. Sai ayyukan ma’aikatan gidaje (household employer activities) da –36.22, da kuma sauran ayyuka (other services) da –20.30.
Dangane da gudunmawar sassa ga jimillar VAT, masana’antu (manufacturing) ne suka fi bayar da kaso mafi girma da kashi 25.89 cikin 100. Sannan bangaren sadarwa da fasahar bayanai (information and communication) ya bayar da kashi 18.77, yayin da hakar ma’adanai (mining and quarrying) ta bayar da kashi 14.85.
A ƙasa kuma, ayyukan ma’aikatan gidaje sun bayar da kaso mafi ƙanƙanta da kashi 0.003 cikin 100. Haka kuma ƙungiyoyin ƙasashen waje (extraterritorial organisations) da bangaren samar da ruwa, magudanar ruwa da kula da shara duk sun bayar da kashi 0.03 cikin 100 kacal.
Rahoton NBS ya nuna cewa tattalin arziƙin ƙasar na ci gaba da nuna alamun bunƙasa a wasu sassa, duk da ƙalubalen da wasu fannoni ke fuskanta.
