Trends

Matatar Dangote Za Ta Fitar da Hannayen Jari Cikin Watanni 5

Attajirin dan kasuwa, Aliko Dangote, ya sanar da cewa ‘yan Najeriya za su iya sayen hannayen jari a Dangote Refinery cikin watanni hudu zuwa biyar masu zuwa, yayin da kamfanin ke shirin shiga kasuwar hada-hadar jari (listing).

Dangote ya bayyana hakan ne lokacin da Shugaban Rukunin Kamfanin Nigerian National Petroleum Company (NNPC), Bayo Ojulari, tare da wasu manyan jami’ai suka kai ziyara matatar man. Ya ce ziyarar na da ma’ana ta musamman, domin NNPC ba kawai abokin hulda ba ne, har ma mai hannun jari ne a matatar.

Ya ce, “NNPC ta zuba jari a lokacin da mu kanmu ba mu da tabbacin nasarar aikin.” Ya kara da cewa sabon jagoranci a NNPC ya kara inganta hadin gwiwa tsakanin bangarorin biyu.

Dangote ya bayyana cewa NNPC na rike da kaso 7.25 cikin 100 na hannayen jarin matatar a madadin ‘yan Najeriya. Ya ce, “Suna rike da kashi 7.25%, wanda ya fi yawan hannayen jarin da Elon Musk ke da su a Tesla.”

Ya tabbatar da cewa masu zuba jari kanana (retail investors) za su samu damar sayen jari kai tsaye nan ba da jimawa ba, tare da bai wa ‘yan Najeriya fifiko. Haka kuma ya ce masu hannun jari za su iya karbar ribar su (dividends) a naira ko dalar Amurka, ganin cewa matatar na samun kudin shiga daga fitar da kayayyaki kasashen waje.

Ana kiyasin darajar matatar man ta kai kimanin dala biliyan 20, kuma ana sa ran shiga kasuwar jari zai kara habaka kasuwar hada-hadar kudi ta Najeriya, da karfafa amincewar masu zuba jari.

Masana sun nuna cewa damar karbar riba a dalar Amurka na iya kare masu zuba jari daga sauyin darajar naira, lamarin da zai sa hannayen jarin su zama masu jan hankali ga kanana da manyan masu zuba jari.

Dangote ya jaddada muhimmancin bai wa jama’a dama, inda ya ce, “Kowane dan Najeriya zai samu damar sayen hannun jari cikin watanni hudu ko biyar masu zuwa.”