Trends

Ramadan: Sarkin Musulmi Ya Ayana Laraba a Matsayin Farkon Azumi

Muhammad Sa’ad Abubakar III, Sarkin Musulmi kuma Shugaban Majalisar Koli ta Harkokin Addinin Musulunci a Najeriya (NSCIA), ya ayyana ranar Laraba, 18 ga Fabrairu, 2026, a matsayin ranar farko ta watan Ramadan 1447 Hijiriyya.

Sanarwar ta biyo bayan tabbatar da ganin jinjirin watan Ramadan a ranar Talata, 17 ga Fabrairu, 2026, wanda ya yi daidai da 29 ga watan Sha’aban 1447AH.

A cikin wata sanarwa da Kwamitin Ba da Shawara kan Harkokin Addini na Majalisar Sultanate ya fitar tare da hadin gwiwar Kwamitin Duban Wata na Kasa, an bayyana cewa an samu rahotanni daga kwamitocin duban wata daban-daban a fadin kasar nan, wadanda suka tabbatar da ganin jinjirin watan.

Bisa ga sahihan rahotannin da aka tantance, Sarkin Musulmi ya amince da shawarwarin da aka gabatar masa, tare da ayyana ranar Laraba, 18 ga Fabrairu, 2026, a matsayin farkon watan Ramadan mai alfarma ga al’ummar Musulmi a Najeriya.

Sanarwar wadda Shugaban Kwamitin Ba da Shawara kan Harkokin Addini, Farfesa Sambo Wali Junaidu, wanda kuma shi ne Wazirin Sakkwato, ya sanya wa hannu, ta isar da sakon taya murna daga Sarkin Musulmi ga daukacin al’ummar Musulmi na Najeriya bisa shigowar wannan wata mai tsarki.

Mai Alfarma Sarkin Musulmi ya bukaci Musulmi su sadaukar da wannan lokaci wajen yin addu’o’i domin zaman lafiya, hadin kai, ci gaba da bunkasar kasa. Haka kuma ya yi addu’ar Allah (SWT) Ya ba da shiriya ga muminai, tare da karbar ibadunsu a cikin wannan wata mai alfarma.

Sarkin Musulmi ya yi wa daukacin Musulmi fatan samun Ramadan mai cike da lada da albarka, tare da rokon Allah Ya zuba albarkarsa a kan kasa baki daya.