Kamfanin Dangote Group ya rattaba hannu kan wata yarjejeniya ta dala miliyan 400 da kamfanin XCMG Construction Machinery Co., Ltd., daya daga cikin manyan masu kera injinan gine-gine a kasar Sin, domin samar da kayan aikin fadada matatar mai.
Yarjejeniyar na daga cikin matakan gaggauta fadada Dangote Petroleum Refinery & Petrochemicals daga karfin tace ganga dubu 650,000 a rana zuwa ganga miliyan 1.4 a rana, wanda zai mayar da ita mafi girman matatar mai a duniya.
A cikin wata sanarwa da kamfanin ya fitar, ya bayyana cewa yarjejeniyar za ta ba shi damar sayen sabbin injinan gine-gine na zamani da za su tallafa wa ayyukan da ake yi yanzu da kuma wadanda ake shirin aiwatarwa a bangarorin tace mai, sinadarai (petrochemicals), noma da kuma manyan ayyukan gine-ginen kasa.
Kamfanin ya kara da cewa sabbin kayan aikin za su hada karfi da karfe da wadanda ake da su a yanzu domin cimma burin fadada matatar, wanda ake sa ran kammala shi cikin shekaru uku masu zuwa.
Baya ga bangaren tace mai, shirin fadada aikin zai kara yawan samar da sinadarin polypropylene daga tan miliyan 900,000 a shekara zuwa tan miliyan 2.4 a shekara.
Haka kuma, karfin samar da takin urea a Najeriya zai ninka sau uku daga tan miliyan 3 a shekara zuwa tan miliyan 9 a shekara, baya ga karfin tan miliyan 3 a shekara da kamfanin ke da shi a Habasha, lamarin da zai kara karfafa matsayin kamfanin a matsayin mafi girman mai samar da urea a duniya.
Haka zalika, karfin samar da sinadarin Linear Alkyl Benzene (LAB) zai karu zuwa tan 400,000 a shekara, wanda zai mayar da kamfanin mafi girma a Afirka wajen samar da wannan sinadari, tare da kara karfafa wadatar kayayyakin da ake bukata a masana’antar sabulu da kayan tsafta.
Shirin fadadar ya kuma hada da karin karfin samar da man tushe (base oil) a matsayin wani bangare na manyan tsare-tsaren bunkasa ayyukan kamfanin.
