Shugaban Hukumar Kula da Aikin Hajji ta Ƙasa (National Hajj Commission of Nigeria – NAHCON), Farfesa Abdullahi Saleh Usman, wanda aka fi sani da Saleh Pakistan, ya ajiye aikinsa daga muƙamin da yake rike da shi.
Wata majiya mai tushe ta tabbatar da hakan a ranar Litinin, sai dai har zuwa lokacin kammala wannan rahoto, ba a bayyana cikakken dalilin murabus ɗinsa a hukumance ba.
Murabus ɗin Farfesa Saleh ya zo ne a daidai lokacin da ake ci gaba da shirye-shirye da tattaunawar manufofi da suka shafi aikin Hajjin Nijeriya. Har yanzu babu wata sanarwa ta hukuma daga NAHCON ko Gwamnatin Tarayya da ke bayyana dalilan da suka sa ya yanke wannan shawara.
Ƙoƙarin jin ta bakin hukumar bai yi nasara ba, kuma har yanzu ba a san ko an naɗa wani shugaban riƙo ba domin kula da harkokin hukumar.
Ana sa ran samun ƙarin bayani yayin da bayanai ke ci gaba da fitowa.
