Babban Bankin Nijeriya (CBN) da Hukumar Kula da Sadarwa ta Ƙasa (NCC) sun gabatar da shirin gudanar da binciken haɗin gwiwa na kai-tsaye a kai a kai kan bankuna, kamfanonin sadarwa, da masu samar da ayyukan biyan kuɗi, domin shawo kan matsalolin da ake yawan fuskanta na gazawar sayen airtime da data.
Shirin, wanda ke cikin wani daftarin ra’ayi (exposure draft) mai kwanan wata 5 ga Fabrairu, 2026, na da nufin magance ƙorafe-ƙorafen da ke ƙaruwa daga masu amfani da ke fuskantar cire kuɗi daga asusunsu ba tare da samun sabis ɗin da suka biya ba.
A cewar daftarin, za a gudanar da binciken a kowane kwata ko a wasu lokuta da hukumomin suka ga dama, inda zai shafi bankuna, kamfanonin sadarwar wayar hannu, ’yan kasuwa, da duk masu lasisin da NCC ta amince da su.
“CBN da NCC za su gudanar da binciken bin ƙa’idoji na masu ruwa da tsaki, ko tare ko dabam, a kowane kwata ko a wasu lokuta da za a ƙayyade,” in ji takardar.
Tsarin yana da nufin tabbatar da ɗaukar alhaki a dukkan sassan harkar kuɗi da sadarwa, tantance bin yarjejeniyar matakin sabis (Service Level Agreements – SLA), da ƙarfafa kare haƙƙin masu amfani da sabis.
Hukumomin sun kuma shirya tabbatar da cewa kamfanoni masu lasisi kaɗai za su shiga harkar sayar da airtime da data, domin rage matsalolin da ke tasowa daga masu shiga tsakani marasa lasisi.
Muhimmin ginshiƙi a cikin tsarin shi ne kaddamar da tsarin maidowa kuɗi kai-tsaye cikin gaggawa tare da tsauraran lokuta. Duk wata mu’amala da ta gaza dole ne ta haifar da maidowa kuɗi ta atomatik cikin daƙiƙa 30. Haka kuma, an takaita bankuna da yin ƙoƙarin sake aiwatar da mu’amala sau biyu kacal, domin hana cire kuɗi sau da yawa a lokacin da tsarin ke da matsala. Za a kuma sanar da kwastomomi halin da mu’amalarsu ke ciki cikin gaggawa.
Domin ƙara bayyana gaskiya, CBN da NCC sun gabatar da shirin ƙirƙirar wani dandalin sa ido na tsakiya da zai rika bibiyar mu’amalolin da suka gaza, maidowa kuɗi, karya SLA, da ƙorafe-ƙorafen masu amfani a ainihin lokaci.
Bugu da ƙari, za a tilasta wa bankuna da kamfanonin sadarwa wallafa rahoton bin SLA a kowane kwata. Tsarin ya kuma bai wa CBN da NCC ikon sanya takunkumi da hukunci kan duk wanda ya karya ƙa’idojin, domin ƙarfafa aiwatar da doka fiye da bin ƙa’ida na son rai.
Jami’ai sun ce aiwatar da wannan tsari zai taimaka wajen dawo da amincewar jama’a ga hanyoyin sayen airtime da data ta dijital a Nijeriya.
