Tsarin Kiwon Lafiyarmu na Fuskantar Manyan Sauye-Sauye – Pate

Ministan Lafiya Farfesa Mohammed Ali Pate

Sashen kiwon lafiya a Najeriya na ci gaba da fuskantar manyan sauye-sauye da jami’an gwamnati ke cewa za su sake fasalta tsarin gaba ɗaya tare da ƙarfafa tattalin arziƙin ƙasar.

Ministan Haɗin Gwiwa na Lafiya da Jinƙai, Farfesa Ali Pate, da Ministan Haɗin Gwiwa na Tattalin Arziƙi, Wale Edun, sun bayyana hakan ne a yayin rattaba hannu kan wata muhimmiyar yarjejeniya ta faɗaɗa kiwon lafiya da aka gudanar a Abuja.

Yarjejeniyar, wadda ta haɗa da International Finance Corporation (IFC), Nigeria Sovereign Investment Authority (NSIA) da MedServe, na da nufin ƙarfafa isar da ayyukan kiwon lafiya ta hanyar jawo jarin masu zaman kansu da kuma faɗaɗa samun ingantaccen kulawa ga ’yan ƙasa.

Pate ya bayyana haɗin gwiwar a matsayin wani muhimmin sauyi. “Tsarin muhalli a Najeriya na canzawa gaba ɗaya, kasuwa na canzawa, haka ma sashen kiwon lafiya na canzawa,” in ji shi.

Ya yi hasashen cewa kafin ƙarshen zangon mulki na biyu na Shugaba Bola Tinubu, sashen kiwon lafiya zai ba da gudunmawa mafi girma ga GDP, tare da kusantar cimma manufar samun cikakken inshorar lafiya ga kowa da kowa.

Ministan ya kuma nuna alamun inganta yawon buɗe ido na kiwon lafiya (medical tourism). “Yawan ’yan Najeriya da ke fita ƙasashen waje domin neman magani ya ragu da kusan rabin adadi, sannan kuma wasu daga waje na zuwa Najeriya domin yawon neman magani. Duk da abin da ake ji game da inganci, gaskiya al’amura na inganta,” in ji Pate.

A nasa jawabin, Edun ya jaddada muhimmancin tattalin arziƙin sashen kiwon lafiya. “Sashen kiwon lafiya injin tattalin arziƙi ne, balle muhimmancin lafiyayyen al’umma,” in ji shi.

Ya ƙara da cewa, “Akwai wasu bangarori da ke tattare da shi da za su taimaka wajen haɓaka GDP, lamarin da ke sa kiwon lafiya ya zama muhimmin ginshiƙi na sabuwar tattalin arziƙin Najeriya.”

Ministocin sun yaba da jagorancin NSIA da kuma haɗin gwiwarta da IFC da sauran abokan hulɗa, tare da kira da a kwaikwayi irin wannan tsari a sauran sassa daban-daban na tattalin arziƙi.
A cewar Pate, yarjejeniyar za ta samar da ayyukan gwaje-gwaje masu araha, kula da cutar daji (onkoloji), da kuma cututtukan zuciya (kardioloji) a faɗin ƙasar nan.

Ya jaddada cewa kiwon lafiya ba kawai hidimar jinƙai ba ce, har ila yau fanni ne na bunƙasar tattalin arziƙi, yana mai cewa sama da kashi 70 cikin 100 na kuɗaɗen da ake kashewa a harkar kiwon lafiya a Najeriya na fitowa ne daga sashen masu zaman kansu.

Ya kammala da cewa ana ci gaba da aiwatar da gyare-gyare don inganta tsarin kuɗaɗen kiwon lafiya, faɗaɗa inshorar lafiya, da jawo ƙarin jarin masu zuba jari, yana mai cewa waɗannan matakai za su shafi rayukan jama’a kai tsaye, su samar da ayyukan yi, tare da ƙarfafa gine-ginen kiwon lafiyar Najeriya.